MAI TAIMAKAWA GWAMNAN KATSINA YA CACCAKI SANATA BARKIYA

0

MAI TAIMAKAWA GWAMNAN KATSINA YA CACCAKI SANATA BARKIYA.


@ Katsina city news
Alhaji Tanimu sada mai taimakawa gwamnan katsina akan walwala da jin dadi ya jawo hankalin sanata kabir barkiya, sanata mai wakiltar katsina ta tsakiya akan ya tuna wahalar da aka sha kafin jama a su zabe shi.
Alhaji tanimu sada yayi wannan rubutun ne a shafin kashin kansa na Facebook a ranar jumma a data gabata.
Tanimu sada yace ya kamata sanata ya sani su da suka sha wahalar tallar shi kuma suke zaune cikin jama a ana masu maganganu sosai maras dadi akan yadda sanatan ke tafiyar da al a murransa.
Tanimu sada yayi Kira ga sanatan ya saurari koke da jama a kuma ya rika bin kafafen yada labarai don jin me ake fadi game dashi.
Katsina city news ta gano yankin katsina ta tsakiya basu taba rashin more sanata ba kamar yanzu.
Dan sanatan shine mai taimaka masa, matar sanatan kuma itace ke duk wasu kwangilar da ake yi na ofishin sanatan karkashin wata gidauniya da take shugabanci.
Yan siyasa na koken cewa ko yaushe sanatan is busy and not reachable.@ katsina city news
Www.katsinacitynews.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here