YAN BINDIGA SUNYI GARKUWA DA WANI BAWAN ALLAH A BATSARI.

0

‘YAN BINDIGA SUNYI GARKUWA DA WANI BAWAN ALLAH A BATSARI.
@ jaridar taskar labarai
Da yammacin ranar lahadi 11-10-2020 da misalin karfe biyar 5:00pm wasu masu garkuwa da mutane ne sukayi awon gaba da wani bawan Allah mai suna Kabir Isah .
Kabir isah ma’aikacin kiwon lafiya ne na Karamar hukubmar Batsari, sun tafi dashi akan hanyar shi ta dawowa daga Jibiya zuwa Batsar.
Bayan sun tafi dashi sun bar babur dinshi da takalmin shi bakin hanya, sannan suka bashi dama ya kira waya ya sanar ma danginshi halin da ya samu kanshi.
hanyar tayi kauran suna wajen yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa domin ko a satin da ya gabata sunyi garkuwa da wasu masu aikin gona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here