KISAN GILLA AKAN WASU FULANI A WURMA
@ jaridar taskar labarai
Wasu yan sa kai daga kananan hukumomin safana, Batsari, da kurfi a jahar katsina sunyi ma wasu fulani wadanda ake zargi suna a cikin wadanda ke a daji suna aikata ta addacin satar mutane, fyade da kisan kiyashi.
Wasu hotuna da jaridun taskar labarai suka samu sun nuna yadda wasu fulanin a kwankwance a bakin ofishin yan sanda na garin kurfi.
Wasu hotunan kuma sun nuna gawarwakin wasu wadanda ake zargin a cikin daji .wadanda ba a San wa ya halaka su ba. Sai dai ana zargin wasu yan sa kai ne, suka aikata aika aikan.
Binciken mu ya gano, wasu da barayin daji suka matsa masu a karamar hukumar kurfi.sune suka gayyato yan sa kai daga kananan hukumomin safana da batsari suzo su taimaka masu.
Yan sakan da suka kawo dauki, sun je kasuwar wurma dake karamar hukumar kurfi a jiya litinin wadda itace ranar kasuwa.inda suka zakulo wasu da ake zargi.
Daga nan aka wuce da su ofishin yan sanda dake kurfi.daga nan kuma anga gawarwakin wasu da ake zargin an masu kisan gilla.wanda ba Wanda ya San wa yayi wannan mummunan aikin.