Gungun Ƴan fashi da makami sun afkawa birnin Kano

0
440

Gungun Ƴan fashi da makami sun afkawa birnin Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

An sami afkuwar fashi da makami aƙalla guda uku a cikin birnin Kano a daren ranar Talata, in ji rahoton Sahelian Times.

Majiyar jaridar ta shaida cewa wasu mutane guda huɗu ɗauke da makamai sun kai hari kantin SHY plaza da ke unguwar Gadon Ƙaya da misalin ƙarfe 8:30 na dare inda suka yi awon gaba da kayayyaki masu daraja.

Daga nan majiyar ta ce ‘yan fashin sun zarce zuwa unguwar Tukuntawa inda a can ma suka yi fashi a wasu shagunan sayar da kaya.

Wani mutum da abin ya faru a kan idonsa, ya bayyanawa Sahelian Times cewa ‘yan bindigar sun zo ne a cikin wata mota ƙirar Golf.

Haka kuma an ce an sake ganinsu a kan titin Bawo da ke unguwar Hausawa inda nan ma suka yi fashi a wasu shaguna.

Ya zuwa yanzu dai rundunar ‘yansanda ta jihar ba ta ce komai ba kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here