Hukumar KANSIEC ta sanya ranar zaɓen ƙananan hukumomi na jihar Kano

0
561

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Shugaban hukumar zaben jihar Kano, Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya shaida wa manema labarai cewa, hukumar KANSIEC ta sanya ranar 16 ga watan Janairun shekarar 2021 a matsayin ranar da za’a gudanar zaben ƙananan hukumomin jihar.

Farfesa Garba Ibrahim Sheka shi ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a shalkwatar hukumar.

Jihar Kano dai na da kananan hukumomi 44, fiye da kowacce jiha a fadin kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here