Gyaran tsarin mulki: INEC na so a sauya tsarin zaɓe daga na hannu zuwa na komfuta

0

 


Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, ya yi kira da a sauya tsarin yadda ake yin zaɓe yanzu daga na hannu zuwa na komfuta, wato ‘electronic system’.

Ya yi wannan kiran ne a wajen taron ƙaddamar da Kwamitin Musamman Na Yi Wa Tsarin Mulkin 1999 Garambawul wanda Majalisar Wakilai ta kafa, a Abuja ran Alhamis.

Farfesa Yakubu ya ce tsarin yadda ake zaɓe a Nijeriya a yau ya zama tsohon yayi matuƙa, wanda saka hannu ya yi yawa cikin sa.

Ya ƙara da cewa lallai ne a yi gyaran da zai bada damar shigo da tsarin yin zaɓe ta hanyar komfuta a cikin tsarin gudanar da zaɓe a ƙasar nan.

Ya ce, “Kun dai Ga nasarar da mu ka samu a Edo inda mu ka samu damar tura sakamakon zaɓe ta hanyar komfuta; saboda haka tilas ne a cire wannan waigin.”

Haka kuma ya yi kira da a kafa hukumar hukunta masu aikata laifuffukan zaɓe, ya na mai ƙarawa da cewa yi wa tsarin mulki kwaskwarima zai bada hanyar da za a riƙa bi ana hukunta masu aikata laifuffuka a lokacin zaɓe a ƙasar nan.

Ya ce akwai kwamitoci da dama a baya waɗanda su ka yi ƙoƙarin ganin an kafa hukumar hukunta masu aikata laifuffukan zaɓe, amma haƙar su ba ta cimma ruwa ba.

Yakubu ya ce kafin a yi babban zaɓen shekarar 2015, INEC ta fito da wani tsari na musamman wanda ya sharɗanta cewa za a riƙa gudanar da zaɓe ne a ranar Asabar ta biyu ta watan Fabrairu.

A cewar sa, haka ake yi a Amurka da Ghana inda su ke da rana ta musamman da su ka keɓe don gudanar da zaɓe.

Ya ce, “Idan aka ɗauki wannan matakin, daga yau zai kasance sauran kwana 855 kafin babban zaɓe kenan; saboda haka ba mu da isasshen lokacin da za a yi wa tsarin mulkin garambawul.”

Babban baƙo mai jawabi a taron, Farfesa Dakas Dakas, ya yi ga kwamitin da ya dubi al’amurran bai wa jama’ar ƙasa damar tofa albarkacin bakin su, da batun sake fasalin zamantakewar siyasar ƙasar, da kuma batun karɓa-karɓar mulki, da sauran su.

Ya yi kira ga kwamitin da ya tabbatar a aikin garambawul ɗin sun samar da tsarin mulkin da zai kasance da gaske na ‘yan Nijeriya ne.

Ya ƙara da cewa muhimmancin samar da tsarin mulki wanda kowa zai yi na’am da shi babban lamari ne wajen ɗorewar Nijeriya.

Dakas, wanda farfesan ilimin shari’a ne, ya yi kira ga ‘yan majalisar da su guji faɗawa cikin matsaloli a ƙoƙarin su na yi wa tsarin mulkin 1999 kwaskwarima, ya na mai nanata cewa su fi maida hankali wajen ganin sun samar da tsarin mulki na dukkan jama’a.

Ya jaddada cewa buƙatar da ke akwai ta tabbatar da cewa akwai sa hannun kowa tare da saka wa kowa shauƙin amincewa da aikin da za a yi shi zai samar da nasara.

Ya ƙara da cewa tilas ne a kauce wa kurakuran da aka yi a baya.

Ya ce, “Ganin cewa a baya wajen aikin yi wa tsarin mulki garambawul mun ci karo da yunƙurin cusa ajandar tazarce karo na uku, wanda a ƙarshe ya rusa dukkan aikin, yanzu akwai ‘yan Nijeriya da dama da su ke tunanin ko akwai buƙatar yin shi wannan aikin.

“Saboda haka, akwai buƙatar a sa ‘yan Nijeriya su aminta da aikin kuma a nuna masu cewa za a yi aiki ne mai aminci kuma wanda ya yi daidai da buƙatun su.”

Ya ce akwai buƙatar a samu goyon bayan kafafen yaɗa labarai, na gargajiya da kuma soshiyal midiya, ya ƙara da cewa ya dace kwamitin ya sadu da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da ƙungiyoyi masu zaman kan su (CSOs).

Haka kuma Dakas ya ce kwamitin ya haɗu da ƙungiyoyin addini, da Majalisun Dokoki na jihohi da sauran manyan masu ruwa da tsaki domin samun ra’ayoyin su kan aikin garambawul ɗin.

Ya ce tilas ne a yi watsi da ra’ayoyi marasa kangado da na son rai, ya ƙara da cewa kada a bari batun addini da na ƙabilanci su shigo cikin aikin.

A cewar sa, “Kada ku wuce gona da iri a fasalin tsarin mulki, sannan ku guji girman kai na giyar mulki ta hanyar kafa misali da ƙarfin misalin ku, ba kafa misali da ƙarfin mulkin ku ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here