Sadiya Umar Farouq za ta jagoranci yekuwar rage faruwar gobara

0

Sadiya Umar Farouq za ta jagoranci yekuwar rage faruwar gobara

Gwamnatin Tarayya za ta fara wata yekuwa kwanan nan kan matakan rage faruwar bala’o’i a wuraren zaman jama’a da ma’aikatun gwamnati.

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce bayyana haka a ranar Laraba a bikin Ranar Rage Aukuwar Bala’i ta Duniya ta shekarar 2020 wanda a kan yi a duk faɗin duniya a kowace ranar 13 ga Oktoba.

A cewar Hajiya Sadiya, za a yi yekuwar ne don ƙara faɗakar da kamfanoni da ma’aikatu da ma sauran jama’ar ƙasa game da yadda za su kasance cikin shirin ko-ta-kwana tare da ɗaukar ɓatakai don rage aukuwar bala’in gobara a dogayen benaye da gidajen masu yawan mutane da gine-gine mallakar jama’a da na gwamnati, da kuma wuraren aiki don tabbatar da cewa sun fito da tsarin ceton jama’a daga gobara tare da yin atisaye jefi-jefi kan yadda za a fice daga inda gobara ta ɓarke.

Ministar ta ce, “Don tabbatar da hakan, wannan Ma’aikatar tare da haɗin gwiwar hukumomin da aka ɗora wa alhakin kula da faruwar bala’o’i, za ta shirya atisaye na farko kan aikin ceto daga gobara a Ginin Sakatariyar Tarayya. Za a yi atisayen a ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2020.

“Za a yi hakan ne domin a cikin shekarar 2020 kaɗai, Nijeriya ta gamu da bala’in gobara sama da guda ashirin a gine-ginen gwamnati da na jama’a.  Saboda haka gobara na daga cikin manyan bala’o’in da ake da su a Nijeriya.

“Manufar atisayen ceto daga gobara da za a yi a makon gobe ita ce a tabbatar da cewa an yi shirin amfani da hanyoyin ficewa daga Ginin Sakatariyar Tarayya idan gobara ta kama shi. Irin wannan atisayen zai bada damar ficewa cikin natsuwa tare da kauce wa rububi da hayaniya da akan yi a lokacin gobara, wanda hakan ya na jawo rasa rayuwa idan babban bala’in gobara ya faru.

“A yayin da hankulan mu su ka koma kan matsalar gobara a wannan rana, wannan Ma’aikata za ta ci gaba da fito da dabaru waɗanda ba kawai faruwar ɗaiɗaikun bala’o’i irin su gobara da ambaliyar ruwa za su yi aiki a kan su ba, har ma da waɗanda kan faru a wasu keɓantattun yanayi kamar bala’i a ma’aikatu irin su fashewar bututun mai da hujewar bututun iskar gas.”

Hajiya Sadiya ta yi kira ga jama’a da su sanar da iyalan su da ofis-ofis ɗin su darussan da za su koya daga atisayen da za a yi kan ceto daga gobara a mako mai zuwa, don ganin an magance aukuwar bala’i a Nijeriya.

Jigon bikin na bana dai shi ne, “Aikin Rage Aukuwar Bala’i”.

Tun daga lokacin da aka ƙirƙiro ta a ranar 21 ga Agusta, 2019, wannan Ma’aikata ta yi ta fito da tsare-tsare da shirye-shirye waɗanda za su taimaka wajen rage faruwar bala’i ko raɗaɗin sa a Nijeriya. Atisayen ceto daga gobara ma zai gaggauta tabbatar da tsarin rage bala’i a ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here