WANENE SAIFULLAHI MIKAILU MATO…?
Dan takarar shugaban NYCN ta jahar katsina?
An haifeni a garin Makera, a karamar hukumar Kankara.A shekarar 1986. A 1990 aka zabi Mahaifina a matsayin shugaban karamar hukumar Kankara a karkashin tsohuwar Jam’iyar SDP, Kafin rasuwar Mahaifina a watan November, 2012 . shine sarkin malaman katsina, sarautar da yanzu take hannun Alh. Aminu Danbaba.
Nayi Makarantar primary a Nuhu model primary school Kankara a 1998, na wuce Karamar sakandire ta GRBSS Kankara na gama a 2001, na dawo garin Katsina a 2001 don cigaba da karatun sakandire a Katsina College Katsina (KCK) a 2001-2004.
A shekarar 2005/6 na samu aikin soja, amma bayan na gama training wasu dalilai na rashin lafiya yasa ban cigaba ba.
Sai a karshen shekarar 2006 na dawo gida na shiga harkar siyasa har nayi takarar kansila a Kankara A & B karkashin jam’iyar PDP, daga baya aka bani mukamin sakataren Campaign Organization na MASARI a matakin karamar hukuma. A 2007 na tafi makarantar HUK poly zuwa 2010.
Na fara aiki da Karamar hukumar Kankara, kafin daga bisani in koma LEA Kankara, yanzun haka ina aiki da gwamnatin jiha tun a shekarar 2014, daga bisani na tafi karo karatu a matakin Degree a UMYUK a 2015 na gama 2019 a fannin turanci da malanta.
Na taba rike mukamin sakataren scholarship na karamar hukumar Kankara, na rike sakataren kungiyar dalibai yan asalin karamar hukumar Kankara dake karatu a HUK poly a 2008, na taba takarar Financial secretary na SUG a HUK Poly a 2009, na rike PRO na kungiyar daliban karamar hukumar Kankara na kasa baki daya, daga baya na rike sakataren kungiyar. Na rike sakataren kungiyar matasa ta Kankara Youth Initiative Forum (KAYIF) zuwa yau, na taba rike sakataren Kankara Youth Progressive movement Association (KAYOPMA) , daga baya aka zabe ni a matsayin chairman na kungiyar. Gwamnatin jihar Katsina ta taba nada ni member a kwamitin tantance ma’aikata 2016.
Na taba jagorantar kungiyar korarrun ma’aikatan kananan hukumomi ta jihar katsina (SOS-FORUM) su 3500 wanda Gwamnatin Shema a 2012 ta taba kora aiki ba bisa ka’ida ba, wannan yasa nayi karar gwamnatin jiha a National Industrial Court, Kano. Daga baya Gwamnatin APC ta Alhaji Aminu Bello Masari ta sanya na janye shariar kuma ta maida ma’aikatan aiki.
wannan gwagwarmayar tasa na zama member a kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International Nigeria. Ina kuma wakiltar kungiyar tallafawa marayu da marasa karfi ta MANUNIYA FOUNDATION dake Kaduna.
Na taba rike mukamin mataimakin sakataren kungiyar GIZAGAWA na jihar Katsina a 2009, a 2014 muka kafa kungiyar Katsina State Social Media Forum inda na rike mukamin sakataren ta har zuwa 2017. Na zama member na kungiyar masu sayar da kasidu ta jihar katsina tun 2012 zuwa yau. karamar hukumar kankara a 2013 ta nada ni PRO na YOUTH COUNCIL daga baya kuma ta turo ni jiha.
Haka fannin sana’o’i ni sanannan kafintane, kuma mai sayar da katako dake da kamfani, baya ga shagon sayar da Jarida da dinki da nike dashi. Nine mai shafin dandali. na DIRECT TO LEADERS, wanda muke da group a WhatsApp da Facebook da sauran platform na social media.
A kananan sana’o’i kuma nayi tireda, na sayar da lemun bawo, na kuma yi sana’ar sayar da doya. Kafin daga bisani sauyin rayuwa yazo.
Bayan an kafa Jam’iyar APC a 2014 na tsaya takarar shugaban Matasa na Jamiya a matakin karamar hukuma amma banyi nasara ba, daga baya kuma na tsaya na jiha, nan ma banyi nasara ba, na taba neman takarar shugabancin karamar hukumar kankara tun 2016 wanda har yau ba’ayi zaben ba, na fito neman Kujerar majalisar jiha a 2019 ,na janye saboda wasu dalilai.
A rubutun gaba zan kawo tsare tsare na ga matasa jahar katsina in an zAbe ni
Ina da iyali.