YAN SANDA SUN TSARE MAWAKI HAMISU BREAKER

0
SHAHARARREN mawaƙin nan wanda tauraruwar sa ke matuƙar haskawa, Hamisu Breaker Ɗorayi, ya shiga hannun ‘yansanda a Kano a bisa zargin dukan kawo wuƙa da wani abokin sa ya yi wa wani mutum.
Binciken mujallar Fim ya gano cewa hatsaniyar ta samo asali ne a ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2020, lokacin da Breaker ya ke tuƙa wata mota ƙirar Toyota tare da wani abokin sa mai suna Abdulzahir ne, sai su ka gogar wa wani mutum mota.
Da aka firfito ana maida magana sai kawai abokin mawaƙin ya shiga jibgar mai motar.
Washegari, wanda aka gogar wa motar, mai suna Sani Kamal Muhammad, ya shaida wa mujallar Fim yadda abin ya faru, ya ce, “Na taho daga hanyar Zoo Road sai na ji wata mota ta goge ni. Ina fitowa, sai na ga Hamisu Breaker da wani abokin sa.
“Abokin nasa ya na fitowa daga motar sai ya fara kutufa ta, ya na dukan karan hanci na. Jini ya na zuba a jiki na. Ya na kuma ta maganganu, har ya ke cewa shi in ya nunan ɓacin ran sa sai ya sumar da ni a nan.”
Can jama’a ta taru, sai aka nemi Breaker aka rasa, ashe ya sulale ya bar wajen lokacin da ya ga abin da Abdulzahir ya aikata. Ana jin ya gudu ne saboda tunanin idan mutane su ka taru da yawa, za a iya ji masa ciwo a cikin dandazon ganin sa.
Daga bisani, ‘yansandan MTD sun shiga cikin maganar bayan Sani ya shigar da ƙara.
Da ma sun riga sun yi awon gaba da Abdulzahir, su ka aje shi a bayan kanta. Haka kuma sun tilasta wa Breaker da ya bayyana a gaban su, kuma ta yi hakan.
Sai dai Breaker ya ce duk rashin haƙuri ne ya jawo matsalar.
Ya faɗa wa mujallar Fim a ofishin ‘yansandan cewa, “Jiya mun gogi motar wani sau ɗaya inda kuma na fito ina ba shi haƙuri. Kuma na fuskanci ya na da zafin rai gaskiya. Mun ba shi haƙuri, ya ƙi hakura, ya haɗe mu ma ga baki ɗaya ya zaga.
“Ka ga kuma in ka zagi wani zai bar ka, wani kuma ba zai bar ka ba. Kuma aboki na ne a gefe, shi ne mai motar tunda ba da mota ta na fita ba, ta na gareji. Shi ne sai ya fito su ka kaure da faɗa.”
Da mujallar Fim ta waiwayi wanda ake zargi kan maganar, wato Abdulzahir, sai ya bayyana cewa, “Bayan na fita na ga irin abin da ya yi mana na gugar bamba, sai na ce Hamisu ya ban motar. To wannan maganar da na yi ne wai ta ɓata mai rai, sai ya fara cuccusa mana ashar, ya na zagi na. Sai na ce, ‘Me ya sa ka ke zagi?’ Ina matsawa kusa da shi sai na ga ya soko min naushi!”
A kan dukan Sani da ya yi har jini na zuba ta hanci kuwa, Abdulzahir ya ce, ”Ai don ma ban fusata ba ne, shi ya sa dukan ya tsaya a wannan yanayi da ake ciki; amma da na fusata, da wani zancen ake yi na daban!”
‘Yansanda dai sun ba su damar yin sulhu.
Game da yiwuwar hakan mai ƙara Sani ya ce shi ya fi so ‘yansanda su kai su kotu don a nema masa haƙƙin sa. Ya faɗa wa wakilin mu cewa, “Ai ba batun masalaha” saboda duk da yake Abdulzahir ya ga jini ya na zuba a jikin sa, “bai nuna nadama ba.”
A yau Juma’a, wakilin mu ya kikkira wayar Hamisu Breaker don ya ji idan an bada belin su, amma ya dinga jin ta a kashe.
Saboda haka yanzu babu tabbacin an sake su ko kuma an ci gaba da tsare su sai zuwa Litinin a kai su kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here