BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SANATA AHMAD BABBA KAITA

0

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SANATA AHMAD BABBA KAITA

*Nazarin Taskar Labarai

Mai daraja Sanata Ahmad Babba Kaita, mun karanta wata wasikar da ke yawo a Yanar Gizo, wadda shafukan jaridun Taskar Labarai suka buga. Bayan mun karanta, tunanin farko da ya zo mana shi ne, kutse aka yi wa shafinka, amma da muka ga ba ka karyata ba, sai muka sakankance a kan cewa kai ka rubutata.

Gaskiya ka yi kuskuren wannan rubutun, kuma basirarka ta bace lokacin da ka wallafa ta. Tabbas wasu za su jinjina maka bisa wasu dalilai.

Tambayarmu a kan ka ita ce; wacce rawa ka taka wajen hana rushe zababbun Ciyamomi a 2015, wanda shi ne tushen matsalar da ake ciki har yanzu?

Wacce rawa ka taka da za a nada Kantomomin da aka rusa? Wace rawa Kantomomin nan suka taka wajen zaben cike gurbi da ka lashe a 2019?

Wacce rawa ka taka wajen zuwa Kotun Koli don ganin ta yanke hukuncin da ke gabanta a kan zaben Kananan Hukumomin Katsina don a wuce wurin a ci gaba a Jihar?

Sanata ba ka da damar ganin Gwamnan Katsina ne? Sau nawa ka yi masa maganar zaben Kananan Hukumomi kai da shi?

Kai ne Sanata mai wakiltar yankin Shugaban Kasa, ka taba maganar da shi? Me ka fada masa? Me ya ce maka?

Sanata mun tabbatar da siyasar yankin Daura tana shirin kwace maka, anya wannan maganar taka ba hau din siyasa ba ne?

Sanata ka yi maganganu da barazanar tunzura jama’a, kana ganin wannan ya dace a Jiha kamar Katsina da ’yan ta’adda ke mata dauki dai-dai?

Mu a Taskar Labarai, muna gani ka yi kuskure a rubutun can, ya kamata ka yi gaggawar janye shi da neman gafara.
_______________________________________________

Ana buga Taskar Labarai a shafin www.taskarlabarai.com da sauran shafukan www.katsinacitynews.com da www.thelinksnews.com. Duk sako a aiko ga 0704 377 7779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here