SANATA AHMAD BABA KAITA YA GARGADI GWAMNATIN JAHAR KATSINA.

0

SANATA AHMAD BABA KAITA YA GARGADI GWAMNATIN JAHAR KATSINA.
daga shafin sa na Facebook
@ katsina city news
Sanata Ahmad babba kaita, sanata mai wakiltar shiyyar Daura yayi wani rubutu a shafin sa na Facebook . Inda yayi Kira ga gwamnatin katsina da kar ta kuskura tace zata nada kantomomi a kananan hukumomi. Ga cikakken rubutun da ya wallafa a shafin nasa. Kamar yadda ya rubuta…ba tare da an gyara ko an cire komai ba.

Raderadi nata gewayawa a jihar akan cewa za’a sake qaqubawa al’ummar jihar kantomomi a qananan hukumominta 34.

Idan har hakan gaskiya ne Ina kira da babbar murya da kada gwamnati ta kuskura ta dauki kawaici da hakurin katsinawa ya zamo abin reni, domin mutane sun gaji kuma bazasu kara lamunce wa gwamnati yi masu irin duk cin kashin data ga dama ba. abinda ke faruwa yau a cikin nigeria ya ishi mai hankali ishara.
Nasan zaku fahimci inda na nufa.

Kada gwamnati ta biyewa masu son zuciya da kwane kwane don cimma wata manufa ko buri na siyasa yin hakan ba zai haifar mata ‘da mai ido ba.
Mutane suna cikin mawuyacin hali a yau din nan duk kau da cewa gwamnatin tarayya tana sakin kudaden local government duk watan duniya, maimakon ayi zabe dukiyar al’umma ta gangara garesu an bar mutane cikin mummunan talauci da kuma fargabar tsaro kuma bamu san inda kudin qananan hukomomin ke zurarewa ba.

Bayan ba gwamnati haqqinta na shawara hawan hawa ba sau daya ba ba sau biyu ba to abun dai yazo karshe ba zamu kara yarda da caretaker chairmen ba domin ya sabawa duk wasu dokokin kasa … ya kamata kuma ‘yan majalisa jiha su tsaya tsayin daka don ganin anyi zabe su kuma sani cewa al’umma na kallonsu kuma Allah (swa) na kallonsu saboda haka ku yarda ‘dan Mangwaro ku huta da quda.

In kuma har kuka bari ba ai zabe ba don za’a baku ku kawo kantomomi to zaku hadu da fushin talakawa domin kune masu laifin …. kuma ko babu komi za’a dawo masu neman quri’a don 2023 kamar gobe ce, ku bar mutane su darje wanda suke ganin zai iya kawo masu cigaba a yankunan su wanan itace demokaradiyya.
Dabara bata bada kujera Allah ne mai bada kujera mui kuma dogon tunani da nazari cewa shin in mun bar kujerar yaya mu keso tarihi ya tuna damu?.

Ita kanta gwamnati sai da ta ciji yatsa kan irin ta’asar da wasu kantomomin suka tabka wancan karon toh don mi zamu koma gidan jiya ?

Duk da mafi yawancin gwamnnonin APC sun tabka abun kunya kan maganar zaben qananan hukumomi bayan zargin PDP da yin rubda ciki da kuma sama da fadi da dukiyar al’umma ta dalilin qin yin zabe, amma duk da haka wadan sunsu sun ‘dan yi hopbasa har su kai zabubuka biyu biyu kai wasu jihohin har ukku ukku bayan da koke koken al’umma ya hana su zaman lafiya, amma banda jihar mu ta katsina duk kau da cewa jihar shugaban kasa ce duk kuma da cewa ya bayyana matsayarshi qarara kan zaben qananan hukumomi.

Babu sauran labewa da maganar kotu domin babu wata jiha wadda bata kotu kan maganar zaben qananan hukumomi (wasu rigingimun na qananan hukomomin tun 2003 suke) amma kuma suka murje idanu su kai zaben saboda dama abinda constitution yay tanadi kenan, sai dai in zuwa kotun kawai anyi ne don a taimaki lauyoyi da alqalai samun kudi.

“IN KUNNE YAJI JIKI YA TSIRA”
SHARHIN MU.
Wannan shine rubutun sanata Ahmad babba kaita. Mu a dakin labarai na katsina city news tambayar mu itace, shin sanata baya da wata danganta da gwamnatin jaha da ba zai iya fada mata ido da ido ba..? Ko ya rubuta ya kai, kai tsaye? Shine sanata mai wakiltar yankin da shugaban kasa ya fito.yana iya ganin shugaban kasa.ya kuma Sanya shugaban kasa yayi ma gwamnan sa magana.? Me ye zafi sanata magana a shafin Facebook? Shine sanatan da ya fi daure ma shugaban jam iyya kugu a Sarrafa jam iyyar APC ta katsina a yadda yake so.ba tare da bin tsarin mulkin jam iyya ba .ko tausayi da jin kai.
Mu a taskar labarai , muna tababa Anya sanatan baya yana amsar wuta bane daga abokin gasar shi a siyasa.watau arc Ahmad dangiwa? Wanda ya kwace masa siyasar kankia , ya kuma hana ma siyasar sa ta yankin funtua zaman lafiya?
Anya Anya sanata da rubutun mai kama da tunzura jama a. Kai talakkawa kar a Raina maku hankali. Da sanata Ahmad babba da gwamnatin katsina kwaryar sama ce data kasa .duk Wanda kuka ji yana wani gunguni.kansa yake mawa wata bukata yake nema ya cimma ta.
______________________________________________
Katsina city news, jarida ce mai zaman kanta dake bisa yanar gizo www.katsinacitynews.com. tana da yar uwarta ta hausa jaridar taskar labarai dake a www.taskarlabarai.com da ta turanci dake a www.thelinksnews.com. duk sako da waya a Kira ko sako ga 07043777779.email katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here