Al’ummar Barwa sun yaba wa minista Sadiya saboda rijiyar burtsatse da asibiti

0

Al’ummar Barwa sun yaba wa minista Sadiya saboda rijiyar burtsatse da asibiti

Al’ummar ƙauyen Barwa da ke Yankin Birnin Tarayya (FCT) sun yaba wa Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya saboda ta gina masu asibiti da rijiyar burtsatse don samun ruwan sha.

Mai’unguwar ƙauyen, Cif Monday Kogi, shi ne ya furta yabon a lokacin da Minista Sadiya Umar Farouq da wasu jami’an ma’aikatar su ka je Barwa domin ƙaddamar da bikin Ranar Magance Fatara ta Duniya ta shekarar 2020 wanda aka yi a ranar Asabar.

Cif Kogi, wanda ya bayyana godiya ga Gwamnatin Tarayya, ya tuno da cewa ƙauyen ba ya da ruwan sha da asibiti har sai da ma’aikatar ta kai masu ziyara a bara.

Ya ce: “Tun zuwan ku na farko a ranar 17 ga Oktoba, 2019, mun ga yadda aka gina mana rijiyar burtsatse da asibiti a ƙauyen Barwa. A madadin jama’ar Barwa, mu na maku godiya.”

Shugaban al’ummar ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta taimaka ta katange asibitin kuma ta gina hanyar zuwa ƙauyen daga filin jirgin sama.

A jawabin ta, Hajiya Sadiya Umar Farouq, wadda Daraktan Harkokin Agaji, Mista Ali Grema ya wakilta, ta ce ta yi murna da ƙaddamar da bikin Ranar Magance Fatara ta Duniya a wannan ƙauyen.

Ta ƙara da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki da hukumomin da ke ƙarƙashin ta don tabbatar da an cimma burin Shugaban Ƙasa na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga fatara a cikin shekara 10.

Ta ce, “Wannan rana ta musamman ta bada dama a fahimci irin ƙoƙari da faman da mutane masu fatara ke yi da kuma damar su faɗi abin da ke damun su.

“An shafe shekaru ana yaƙi da fatara a yayin da kashi arba’in cikin ɗari na al’ummar Nijeriya su na rayuwa ne cikin ƙunci kamar yadda Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta bayyana. Ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnati shi ne a taimaka wa dukkan jama’a kuma a ba su kariyar da ta dace domin yaƙi da fatara abu ne da ke cikin ran gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

“Wannan gwamnatin ta kasance mai sadaukarwa ga manufofi da tsare-tsaren kula da mutane masu ƙaramin ƙarfi na duniya kuma za ta yi aiki da manufofin ƙasa da ƙasa na Majalisar Ɗinkin Duniya.”

Ita dai Ma’aikatar Harkokin Agaji, ta zaɓi ƙauyen Barwa ne a matsayin inda za ta fara wannan bikin na Ranar Magance Fatara ta Duniya a bara tare da taimaka wa ƙauyen ta hanyar gina masu wurin shan magani da kuma sama masu wurin ɗibar ruwan sha ta hanyar shirin taimakon al’umma, wato ‘Community and Social Development Project’ (CSDP).

A bana, ma’aikatar ta bada kyautar wuraren wanke hannu guda uku da kayan wanki da su ka haɗa da sabulai, ƙyallayen rufe fuska da magungunan tsaftace hannu ga iyalai, da kuma tukunyar jama’a saboda wannan ranar, a yayin da ministar da sauran jami’ai su ka yi wankin hannayen su na gwaji ga jama’a.

Jigon bikin na bana dai shi ne “Aiki Tare don Cimna Adalcin Al’umma da Yanayi ga Kowa”, wato ‘Acting Together to Achieve Social and Environmental Justice for All”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here