Yadda Hajiya Sadiya ta kai tallafin gwamnati ga Sokoto saboda ambaliya
Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari saboda agajin gaggawa da ya kai wa al’ummar jihar sakamakon bala’in ambaliyar ruwan sama da aka yi a jihar.
Ambaliyar ta shafi ƙananan hukumomin Gwadabawa, Illela, Sokoto ta Arewa, Wammako, Boɗinga da Tambuwal inda ta lalata gonaki da amfanin gona masu yawan gaske.
Gwamnan ya yi yabon ne a ƙarshen makon jiya lokacin da Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ziyarci jihar domin rarraba kayan agaji tare da ƙaddamar da Shirin Bada Lamuni Ga Matan Karkara, wato ‘Rural Women’s Grant Project’.
Ya ce: “Tilas ne in yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari saboda saƙon alheri, jajantawa da tausayawar da ya yi mana tun farko a kan bala’in da ya faru a garuruwan mu masu yawa, da kuma tallafin da ya ba waɗanda abin ya shafa.
“Mu na aikin fito da wani kasafin kuɗi na musamnan da za mu kai wa Shugaban Ƙasa don ya ga yadda za mu sake gina gidaje, asibitoci da makarantu da ambaliyar ta shafa.
“Mu na kuma yaba wa mai girma Shugaban Ƙasa saboda ayyukan sa na agaza wa jama’a. Akwai su da dama kuma mu na godiya kan yadda Jihar Sokoto ta amfana daga waɗannan shirye-shirye.
“Mu na tabbatar maku da cewa al’umma da gwamnatin Jihar Sokoto a shirye mu ke mu haɗa gwiwa da ku a kowane shiri da zai amfani jama’a.”
Gwamnan, wanda ya bayyana Jihar Sokoto a matsayin jiha mai tanyon mata, ya yi alƙawarin ƙara azama wajen ƙarfafa wa mata, musamman waɗanda ke zaune a yankunan karkara.
Tun da farko, sai da Minista Sadiya Umar Farouq ta jajanta wa gwamnatin jihar a kan bala’in ambaliyar.
Ta ce, “Mai Girma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, GCFR, ya damu da ɓarnar da ambaliyar ta jawo kuma ya bada umarni ga Ma’aikar Harkojin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya da ta sa Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta yi azama wajen samar da taimakon da mutanen da abin ya shafa ke buƙata. Ga ni na zo tare da Darakta Janar na NEMA domin mu kawo kayan agaji da aka amince a rarraba don taimakon waɗanda abin ya shafa.”
Kayan agajin da aka kai wa jihar sun haɗa da buhun masara 1,502, buhun shinkafa 1,502, buhun wake 1,502, garwar manja 107, garwar man girki 43, katan-katan na kayan haɗin girki guda 202, katan 141 na tumatirin gwangwani da kuma buhu 22 na gishiri.
Sauran sun haɗa da bargo 3,868, katifa 3,868, gidan sauro 3,004, buhun siminti 3,780, bandir ɗin kwanon rufi 3,780, buhun ƙusa 723, fakitin ƙusar kwano 200 da kuma katan 72 na omo.
Ministar ta yi la’akari da cewa tun ma kafin a raba waɗannan kayan agajin, Gwamnatin Tarayya ta riga ta tura wasu kayan agajin ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Goronyo da ambaliyar ta shafa, ta hanyar NEMA.
Ta ce, “Ofishin NEMA da ke Sokoto ya gudanar da binciken gani da ido a ƙananan hukumomin Binji da Silame. An amince a kai masu kayan agaji kafin ƙarshen satin nan kamar haka:
i. buhun shinkafa 455 (kilo 12.5)
ii. buhun masara 455 (kilo 12.5)
iii. buhun wake 455 (kilo 25)
iv. katan 76 na kayan haɗin girki 76
v. jarka 46 (lita 20) ta man girki
vi. katan 38 na tumatirin gwangwani
vii. bargo 910
viii. katifa 910
ix. gidan sauro 910
x. buhun siminti 600
xi. bandir 600 na kwanon rufi
xii. fakiti 200 na ƙusar kwanon rufi
xiii. buhu 67 na ƙusa inci 3
Hajiya Sadiya ta kuma bayyana cewa za a riƙa biyan N5,000 a kowane wata ga gidaje 3,465 na mabuƙata a Jihar Sokoto, yayin da ana shirin rubuta gidaje 29,676 na mabuƙata cikin wannan shirin.
Ta yi kira ga gwamnan da ya taimaka wa jihar domin ta shigar da ƙarin mutane cikin shirye-shiryen bada tallafin da ma’aikatar ta ke gudanarwa.
Hajiya Sadiya Umar Farouq na raba N20,000 a Jihar Sokoto a ƙarƙashin Shirin Bada Lamuni ga Matan Karkara
Tarin katifun agaji ga waɗanda ambaliya ta shafa a Jihar Sokoto