Yan sanda a Kano sun cafke lauyan bogi

0

‘Yan sanda a Kano sun cafke lauyan bogi

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Ƙungiyar Lauyoyi ta ƙasa reshen jihar Kano (NBA) ta bayyana cewa sun samu rahoton wani mutum mai suna Muhammad Maina da ya ke sojan gona a matsayin lauya.

Muhammad Maina wanda mazaunin unguwar Tinshama ne da ke yankin Hotoro a ƙaramar hukumar Tarauni da ke jihar Kano, ya na gabatar da kan sa a matsayin lauya tare kuma da karɓar kuɗi a gurin mutane.

Sakataren harkokin shari’a na ƙungiyar ta NBA Barrister Ibrahim Abdullahi Chedi, ne ya sanar da haka a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai,

Barrister Ibrahim Abdullahi Chedi ya ce a daren ranar alhamis din 15 ga watan Oktobar nan wannan mutum mai suna Muhammad Maina, ya karɓi kuɗi daga hannun mutum mai Suna Samuel Odey Felu.

Tun da fari Samuel Odey Felu ya yi korafin yana bin wani mutum bashin kudi kimanin naira miliyan 26, in da ya yi jinga da Muhammad Maina, wanda lauyan bogi ne akan zai karɓa masa waɗannan kuɗi da ya ke bi.

Muhammad Maina ya karɓi jimlar kuɗi naira 600, 000 a matsayin kuɗin aiki sai kuma naira 50, 000 a matsayin kuɗin wata yarjejeniya da ya rubuta masa, sai kuma naira 10,000 a matsayin kuɗin addu’a saboda samun nasara a cikin harkar shari’ar, inda jumlar kuɗi ya tashi naira 660, 000

Tuni dai Muhammad Maina ya faɗa hannun jami’an ƴan sanda na Hotoro, inda ya amsa laifinsa tare da tabbatar da cewa shi ba lauya bane.

Haka kuma Ibrahim Abdullahi Chedi ya ce ƙungiyarsu ta NBA ta shigar da ƙorafi a chaji ofis din ƴan sanda na Hotoro ta hannun wani lauya mai suna A. A Umar wanda aka fi sani da A2, wanda tun asali shi ne ya sanar da ƙungiyar ta NBA batun wannan lauya na bogi, tuni dai jami’an na ƴan sanda su ka tura wannan al’amari zuwa sashen binciken manyan laifuka da ke babbar rundunar ƴan sanda da ta ke Bompai.

A ƙarshe ya ce ƙungiyar ta NBA ta ce za ta cigaba da faɗaɗa bincike akan wannan al’amari domin ɗaukar matakin shari’a akan duk wanda aka samu hannunsa a ciki, haka kuma ta buƙaci al’umma da su dinga kula da waɗanda za su yi mu’amala da shi a matsayin lauya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here