BAKIN TALAUCIN DA WASU SHUGABANNIN JAM’IYYAR APC NA JIHAR KATSINA KE CIKI  

0

BAKIN TALAUCIN DA WASU SHUGABANNIN JAM’IYYAR APC NA JIHAR KATSINA KE CIKI

@Jaridar Taskar Labarai

Wani bangare na halin da jam’iyyar APC ke ciki a Jihar Katsina, shi ne halin bakin talauci wanda wasu daga cikin shugabanninta na Jiha da na Kananan Hukumomi ke ciki.

Wannan rahoton yana cikin bangaren binciken da jaridar TASKAR LABARAI ke yi na halin shugabancin kashin dankali da ko-in-kula da kuma rashin bin tsarin mulkin jam’iyya wanda jam’iyyar APC ta Jihar Katsina ke ciki.

A bincikenmu mun ji labarai masu ban tausayi daga bakunan ’yan jam’iyyar nan. Wasu suna rike da shugabanci a Jiha, wasu a Kananan Hukumominsu.

Bayan kammala zaben Shugaban jam’iyyar a matakin Jiha da na Karamar Hukumomi, Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya tabbatar wa da shugabannin cewa za tafi da su, kuma babu wani Shugaban da zai yi nadama ko ya yi maula. Haka wani daga cikin shugabannin ya tabbatar wa jaridar nan bisa amana a labaran da yake fada mata.

Bincikenmu ya tabbatar mana Gwamnan ya rika ba da kwangila don a siyar a ba shugabannin wani kaso na kudin, amma maimakon a ba su su siyar da kansu, ko su nemo dan kwangilar da zai masu aikin, sai a siyar masu a ba su abin da ya samu.

Wani Shugaban ya shaida wa jaridar nan cewa; “An taba yi mana waya aka ce Gwamna ya ba mu kwangila daga Hukumar Ilmin Firamare ta Jiha, amma aka ce Gwamnan wai ya ce a siyar wa wane da wane. Sai aka rika turo mana wani abu aka ce wai sune kasafinmu bayan an siyar da kwangilolin. Daga baya muka ji cewa kamfanin Marmara Ventures ne ya yi aikin baki dayansa”.

Bincike jaridar nan ya gano daga tsarin taimakon jam’iyya da masu rike da mukamanta akan cire kudi daga albashin duk wani mai rike da mukamin siyasa a Jiha, tun daga mai rike da mukamin mai taimaka wa Gwamna, har zuwa Gwamnan da mataimakinsa.

Bincikenmu ya tabbatar ana cirewa duk wata, amma mun kasa gano ya ake yi da kudin. Da wa da wa ke amfana? Yaushe ake raba su? Ya ake raba su? Don mafi yawan shugabannin da muka tambaya sun ce a tsari da tabbaci ana cirewa, amma bayanin yadda ake yi da su, wannan sai  Shugaban jam’iyya na Jiha, Alhaji Shittu S. Shittu zai iya bayani dalla-dalla.

Duk da wadannan tsare-tsare na samar wa jam’iyyar kudi don a taimaki ’yan jam’iyya, wasu  mutanen suna rayuwa cikin bakin talauci da bara da kuma takaici, kamar yadda bincikenmu ya tabbatar.

Wani abin haushi, yau watanni masu yawa jam’iyyar ba ta kira taro ba, balle a tattauna halin da al’umma ke ciki, har su ma nasu ya samu shiga, balle har a san wane hali, kowa ke ciki.

Mun samu misalai da yawa, amma za mu kawo ukku kacal, sauran za mu kawo su a gaba in halin haka ta bada. Kuma za mu sakaya sunansu, kamar yadda suka bukata.

Babu abin da ya kai Mahaifiya daraja. Wani Shugaba a jam’iyyar APC yana kallo Mahaifiyarsa na juyawar zafin ciwo, Hawaye na zuba a kumatun gyatumarsa ga lissafin magani da kudin gwaje-gwaje na Likitoci, amma ba yadda zai yi tunda ba shi da kudi.

Ya taba aljihunsa, ya duba wayarsa, sai kawai kwalla suka cika masa ido, yana cikin wannan halin matarsa ta dafa kafadarsa tana ba shi hakuri. A cikin hakurin ta kuma fada masa wasu matsalolin cikin gida, amma ta ce; “Mun dauke maka wannan, ka ji da na Hajiya, ko da roko da bara da maula ne ka yi in dai za ka fita kunyar tsohuwar nan.”

Wani Shugaban, Dansa na cikinsa ne ba shi da lafiya, aka rubuto magani babu kudin siya, haka ya yi ta buga waya. Daga nan ya hawo mota ya nufo Katsina ofishin jam’iyya ta Jiha, ba wanda zai gani a wajen. Ya nufin gidan Shugaban jam’iyya, shi kuma ba ya shigo saboda matakan tsaro. Duk wani mai rike da mukami daga Karamar Hukumarsu ya kasa ganin ko daya. Da kyar ya gano wani abokin karatunsa, shi ne ya ji matsalarsa, ya kawo kudi masu kima ya ba shi ya hawo mota. Kafin ya iso garinsu yaron ya rasu.

Wani Shugaba aure zai yi kuma na dole, saboda dolen ta sanya ya yi auren, ga wani ibtila’i ya same shi. Na kusa da shi suka tabbatar cewa saboda dubu 50 ya rasa ina zai same ta, sai dai abokan da suka taso tare suka taimaka masa ya fita daga wannan kangin na rayuwa, amma ba jam’iyyar da ya sadaukar da rayuwarsa a kanta ba.

Bincikenmu ya tabbatar mana mutum uku ne kawai shugabancin Jiha ba su tare da damuwa da bakin cikin hali da abin da ke faruwa.

Wani Shugaban jam’iyya cewa ya yi; “Babu abin da take mana, mune ke fita mu samo abin da muke rike mutanenmu, ka san siyasa sai da jama’a. In ka bari jama’arka suka bar ka, ka yi asara.”

Bincikenmu ya tabbatar mana babu wani Shugaban jam’iyya na Jiha da zai iya yi maka maganin Naira dubu 20 da ya samu daga ribar jam’iyya in ban da mutum uku. Ko na Karamar Hukuma, da zai iya yi maka maganin Naira dubu 10 da ya samu daga jam’iyya. Ko na Unguwa, da zai iya yi maka maganin Naira dubu uku.

Labaran shugabannin nan da aka yi wahala da su yana da ban tausayi. Duk wanda ka samu yana da labarin da zai ba ka mai sosa zuciya.

A wani bangaren binciken mun gano cewa, yayin da bayin Allah nan ke cikin wannnan halin na ban tausayi, wanda ya samu canji a rayuwarsa shi ne Shugaban jam’iyya na Jiha, Alhaji Shitu S. Shitu.

Bincikemu ya gano wasu ayyukan da suka shafi kwangiloli da kawo motoci wadanda duk ana dangantakawa da kamfaninsa, wadanda kudinsu suna da yawan gaske, yawan na fitar hankali.

Wani kamfani da ya yi aikin gina da gyaran makarantu a Hukumar Ilmin Firamare ta Jiha da wanda ya kai motoci a Babbar Kotun Jiha da wasu wurare, duk ana danganta su da kamfanin Shugaban jam’iyya na Jiha.

Duk ’yan jam’iyya da wannan jaridar ta yi hira da su, sun ce duk da wannan fantamawa da Shugaban yake yi, wai babu wani jin kan a zo a gani tsakaninsa da mataimakansa na mulki a jam’iyance.

Shugaban yakan samu gata na masu rike da mukaman da aka zabe su, wadanda sukan kula da shi kulawar gaske, kuma yakan rike kulawar nan ne kawai a kansa.

Mun yi kokarin jin ta bakin Shugaban jam’iyyar APC din na Jihar Katsina, Alhaji Shittu S. Shitu, amma hakar mu ba ta cimma ruwa ba. Mun rubuta masa a rubuce, mun aika masa sakon kar-ta-kwana, mun aika baka da baka, duk yaki kare kansa.
Muna da sauran rahoton da zamu fito dashi,in ya bada nasa bahasin zamu hada mu fitar tare.
________________________________________________
Kamfanin Matasa Media Links, shi ne ke da jaridun Jaridar Taskar Labarai a www.taskarlabarai.com da kuma The Links News awww.thelinksnews.com dawww.katsinacitynews.com.  Duk sako a aiko ga 0704 377 7779, ko Emailkatsinaoffice@yahoo.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here