DA DUMI-DUMI | Wata babbar kotu a jihar Kaduna karkashin jagoranci mai shari’a K Dabo ta dakatar da sabon sarkin Zazzau Amb. Ahmad Nuhu Bamalli daga amsa sunan sarkin Zazzau, har sai ta zauna ta saurari shari’ar da Iyan Zazzau Bashir Aminu ya shigar a gabanta.
Tun a kwanakin baya ne dai Iyan Zazzau ya maka sabon sarkin Zazzau da gwamnatin jihar Kaduna a gaban kotu inda yake kalubalantar hanyar da Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya zama sarkin Zazzau.