YADDA SANATOCI KE WANKA DA MANYAN KUDADE

0

YADDA SANATOCI KE WANKA DA MANYAN KUDADE…DA NI NE..
daga Umar tata

Ya zuwa yanzun ina da tabbacin al’umma masu mu’amulla da facebook sun sani cewa duk Sanata yana daukar N29,479,749 a duk wata sa6anin N13,000,000 da na ce a rubutu na na baya. Wannan kudi ba nashi bane ba shi kadai, a a kudin al’umma ne saboda akwai constituency allowance da akayi monetising tun hawan mulkin shugaba Buhari ana saka ma kowane Sanata a cikin albashin shi duk wata. Shiyasa kudin suka yi yawan haka.

Ni dai in nine Sanatan Katsina ta tsakiya, sanin halin da al’umma ta suke ciki na matsalar tsaro, a shekarar farko zan maida hankali na kacokam wajen tsaro ta hanyar da duk zan iya don kare rayukka, mutunci da dukuyoyin al’ummar gunduma ta. Da wadannan kudin a cikin shekara daya da yardar Allah sai nayi ma tsaro hidima kamar haka:

1) Jibia local government zan sai ma yan sandan Jibia Hilux pick up vans guda 3 da babura 20 sannan duk wata zan baiwa Jibia Divisional Police Station N500,000 don sayen mai da servicing na motocin da baburan. Zan baiwa YAN SAKAI pick up 3 da babura 50 da gudummuwar bindiga PUMP ACTION 100 kamar yanda doka ta yarda cewa kana iya sayen su kayi masu licence don farauta. Zan rinka basu duk wata N1M domin sayen harsashi da servicing na motocin su da baburan su.

2) Batsari local government.
a – Police 3 Hilux Pick up vans
b – 20 motorcycle
c – N500,000 duk wata na hidima

YAN SAKAI
a – 3 hilux pick up vans
b – 50 motorcycle
c – 100 Pump Action licenced guns
d – N1M don sayen harsashi da hidima.

3) Safana local government.
a – Police 3 Hilux Pick up vans
b – 20 motorcycle
c – N500,000 duk wata na hidima

YAN SAKAI
a – 3 hilux pick up vans
b – 50 motorcycle
c – 100 Pump Action licenced guns
d – N1M don sayen harsashi da hidima

4) Kurfi local government
a – Police 3 Hilux Pick up
b – 20 motorcycle
c – N500,000 duk wata na hidima

YAN SAKAI
a – 3 hilux pick up vans
b – 50 motorcycle
c – 100 Pump Action licenced guns
d – N1M don sayen harsashi da hidima

5) Danmusa local government
a – Police 3 Hilux Pick up
b – 20 motorcycle
c – N500,000 duk wata na hidima

YAN SAKAI
a – 3 hilux pick up vans
b – 50 motorcycle
c – 100 Pump Action licenced guns
d – N1M don sayen harsashi da hidima

6) Dutsinma local government
a – Area Command 5 Hilux Pick Up Vans
b – Divisional Police Station 3 Hilux
c – 50 motorcycle
d – N1M

YAN SAKAI
a – 5 Hilux Pick Up Vans
b – 50 motorcycle
c – 100 licenced pump up action guns
d – N1M don sayen harsashi da hidima

Ban ce zan yi takarar Sanata ba, amman tabbas da ace nine wannan shine tsarin da zan maida hankali a kanshi cikin shekarar farko don ganin al’umma ta ta samu tsaro da natsuwa.

Wallahi aikin bai da wahala samun goyon bayan talakka ga mai nufin shi da alkhairi shine babban matsalar. Ina da tabbacin Sanatan mu na yanzun yana da damar yin wannan aikin ko abinda ya fi shi! Kuma na san zai iya don mutumen kirki ne!

Yanda muka dama haka zamu sha!
Umar Tata tsohon Dan takarar gwamna katsina ne a jahar katsina. Kuma yana cikin dattawan jam iyyar APC na jahar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here