Gwamna Ganduje ya taya Sanata Rabi’u Kwankwaso murnar cika shekaru 64 a duniya
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Duk da irin saɓanin siyasar da ke tsakanin gwamnan jihar Kano da tsohon maigidansa a siyasa wato Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, sai ga shi gwamna Ganduje ya yi bazata wajen aikewa da saƙon taya murna ga tsohon maigidan sa.
Gwamna Ganduje ya shiga jerin dubun-dubatar mutanen da su ka taya tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, wato Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
An dai wallafa sakon taya murnar mai ɗauke da sa hannun gwamna Ganduje a jaridar Daily Trust inda yake cewa “a madadina da al’ummar jihar Kano muna taya tsohon gwamnan jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 64 a duniya, muna yi masa fatan tsahon rai da ingantacciyar lafiya”
Tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso da tsohon mataimakinsa kuma gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje sun kwashe shekaru hudu suna jan ragamar jihar Kano wato daga 1999 zuwa 2003, kafin gwamna Ibrahim Shekarau ya kayar da su.
Mutanen biyu sun kwashe shekaru 8 suna aiki tare a gwamnatin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, kafin 2011 lokacin da suka sake samun nasara suka dawo kan karagar mulki,
A shekarar 2015 Kwankwaso ya daga hannun Ganduje inda ya zama gwamnan jihar ta Kano, shekara daya bayan nan ne rashin jituwa tsakanin abokan siyasar biyu ta kunno kai har zuwa 2019, wani lokacin da rikicin ya fi ta’azzara.