Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 22

0

Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 22

Yan bindiga sun hallaka akalla mutane 22 a garin Tungar Kwana dake karamar hukumar Talata-Mafara ta jihar Zamfara daren Talata, 20 ga watan Oktoba, 2020, tare da yin awon gaba da wasu mutanen.

Wani dan garin mai suna Malam Ahmed Mohammed ya bayyanawa manema labarai cewa ‘yan bindiga sama da 100 sun kai farmaki kauyen misalin karfe 11 na dare kuma suka fara harbe-harbe.

“Mutane ashirin da biyu, wanda ya hada da mata da yara aka kashe lokaci guda, yayinda wasu suka gudu cikin daji.” Mohammed ya kara da cewa mutane da dama sun jiggata sakamakon harbi kuma an garzaya da su asibiti domin jinya.

A cewarsa, ‘yan bindigan sun yi awon gaba da dabbobi da yawa. “Sun kwashe mana shanu, tumakai, da awaki da kuma kayan abinci,”.

See also  Dan ta'adda Aleru ya Gana da Mutanan Karamar Hukumar Faskarin Jihar Katsina.

Ya ce mutanen ƙauyen sun gudu daga garin saboda tsoron dawowan ‘yan bindigan saboda sun dade suna kai hari garin ba tare da ɗaukar wani mataki ba.

Da yake tabbatar da haka, kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya ce “Hukumar yan sanda ta tabbatar da kisan mutane 20 amma ba mutane 22 ba.”

Shehu ya ce ‘yan bindigan sun kai harin ne saboda mutanen garin sun baiwa jami’an tsaro bayani kansu wanda yayi sanadiyar kisan da yawa cikinsu.

Ya ce hukumar ‘yan sanda ta tura jami’anta domin damke ‘yan bindigan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here