FCE Kano ta sanar da ranar dawowa Makaranta

0

FCE Kano ta sanar da ranar dawowa Makaranta

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Kwalejin Ilimi ta gwamnatin Tarayya da ke Kano wato FCE, ta sanya ranar Litinin 2 ga watan Nuwamba a matsayin ranar komawa karatu.

Kwalejin ta ce komawar ta shafi masu karatun NCE da yan Part-Time da kuma masu Pre-NCE.

Sanarwar hakan ta fito ne daga wata mataimakin magatakardar kwalejin kuma shugaban sashin hulda da jama’a na kwalejin, Auwalu Mudi Yakasai.

Sanarwar ta ce, hukumar kwalejin na umartar dukkan daliban da za su koma da su bi ƙa’idojin kariya daga cutar COVID-19.

“Ana saran dukkan dalibai za su sanya safar rufe hanci da baki yayin da za su shiga makaranta”, inji sanarwar.

Ya zuwa yanzu an shafe tsawon watanni bakwai makaratu na rufe. A Nijeriya an samu asarar rayukan mutane sama da 1000 a sanadiyar cutar Kurona yayin da ta harbi sama da mutum 59,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here