Fitaccen Mawakin Hausa Alhaji Hassan Wayam ya Rasu

0

Shahararren mawakin Gargajiyar nan Alhaji Hassan Wayam, ya rasu a daren yau da misalin karfe 3:30 na tsakar dare.

Dansa, Bello Hassan Wayam, ne ya tabbatar wa da jaridar LEADERSHIP dazun nan a wata zantawa da shi ta wayar tarho.

Marigayi Hassan Wayam ya rasu ya na da shekaru 76, inda ya bar mata daya da ‘ya’ya 11 da kuma jikoki da dama.
Ya rasu ne a gidansa da ke Zaria a Jihar Kaduna bayan doguwar jinya da ya yi fama da ita.

An yi jana’izarsa a gidansa da ke Zaria kamar yadda addinin musulunci ya tanadar, inda a ka binne shi a makabartar da ke garin.

Kafin rasuwarsa, ya yi shuhura wajen yin wakoki masu cike da hikima da wa’azantarwa. Allah ya gafarta ma sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here