FUSKOKIN MATAN DA SUKA KIRA DA KUMA JOGARANTAR ZANGA-ZANGAR “ENDSARS”

0

FUSKOKIN MATAN DA SUKA KIRA DA KUMA JOGARANTAR ZANGA-ZANGAR “ENDSARS”

Daga Danjuma Katsina

Kungiyar da yi kira kuma ta jagoranci zanga-zangar a kawo karshe rundunar nan ta musamman ta ‘yan sanda mai suna FSARS, ta fitar da wata sanarwa wadda a ciki ta yi kira ga matasa su koma gidajensu domin canza sabon salo.

Kungiyar ta kuma shelanta jingine amsar gudummuwar kudade domin ci gaba da wannan zanga-zangar.

A shelar, kungiyar ta kawo sunayen membobinta da sune suka hadu suka kafa ta, kuma suka rika jagorancin abin da ya faru cikin lumana, kafin ya rikide ya zama babbar fitina.

Kafin wannan shelar dai, Gwamnatin Tarayya da na Jihohi sun rasa da wa za su yi magana, saboda sun ce masu zanga-zangar ba su da shugabanci.

Duk da haka, ana ganin ana kawo abinci mai kyau da ruwa da kuma yin magani ga duk wanda ya ji ciwo a tsanake, wanda ya tabbatar suna da shugabanci, amma a boye.

A shelar, kungiyar ta bayyana yawan kudin da suka tara na gudummuwa da suka kai kusan Naira miliyan 150 daga kasashen duniya, suka kuma yi bayanin yadda suka kashe kudin da sauran abin da ya rage.

Wani abu da jerin sunayen shugabannin kungiyar ta fitar, ya nuna duk mata ne, ba wadda ta kai shekara 40 a cikinsu.

Dukkaninsu mata ne zalla, shi ya sa suka sanya wa kungiyar suna; Hadaddiyar Kungiyoyin Kare Martabar Mata.

Dukkaninsu masana ne a ilmin Yanar Gizo, kuma sun shahar a fasahar zamani, kuma sun dade suna da tasiri a wannan kafa.

Dukkanin su marubuta ne a Yanar Gizo, wasu kuma ‘yan jaridu ne da ke aiki a wasu kafofin a kasashen waje.

Wasu suna da shafukan a Yanar Gizo masu tasirin gaske. Dukkanin su suna da alaka da karatu a kasashen waje, kamar Ingila ko Amurka.

Mafi yawansu manyan Attajiran kansu ne, sun yi suna a fannin da suke, wanda mafi yawa na da alaka da kungiyoyin fadakarwa ko amfani da kafar sadarwa ta zamani.

Suna fara amsar gudummuwa aka rufe asusun ajiyarsu da suke amfani da shi. Cikin awowi suka canza salo amsar kudaden daga kasashen duniya, wanda Gwamnatin Tarayya ba ta iya tarewa.

Dukkanin su ba wanda ya je inda ake zanga-zangar, daga ofisoshinsu da gidajensu, wasu ma daga kasashen wajen suka rika tafiyar da ya za a yi, kuma daga can suka rika aiki da oamintattunsu da ke wajen zanga zangar.

Ga sunayensu kamar yadda kungiyar ta fitar da kanta da a kuma hotonsu kamar yadda muka zakulo maku.
Sunayen sune 1, fakhriyya Hashim.2.laila Johnson salami.3.Damilole adufuwa.4 odanayo eweniyi.5 layo ogunbawo. 6. Ozzy etomi.7 ire aderenokun.8 oluwaseun ayodeji osowobi.9 jola ayaye.10 karo omu. 11.obiageli ofili akanta tito.12.kiki mordi.13 fkk abudu. Ga kuma hutunansu kaf da wannan Rahoton. Tarihi ba zai manta dasu ba. ,Matan da suka jagoranci girgiza gwamnati a shekarar 2020


Danjuma katsina ya rubuta labarin ne ga jaridun taskar labarai da katsina city news. Wadanda ke a www.taskarlabarai.com da www.katsinacitynews.com Kira ko sako 07043777779.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here