KUYI AMFANI DA TSARE TSARENMU NA RAGE FATARA….Shugaban kasa Buhari
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga matasan Nijeriya da su yi amfani da damar da aka ba su cikin shirye-shiryen da gwamnatin sa ta fito da su don rage fatara da rashin aikin yi.
Shirye-shiryen, waɗanda da Turanci ake kira ‘National Social Investment Programmes (NSIPs)’, ana gudanar da su ne a ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya domin a kyautata rayuwar matasan da sauran mabuƙata.
Shugaban ya yi wannan maganar ne a cikin jawabin da ya gabatar ga ƙasar nan kan tarzomar ‘EndSARS’ a daren Alhamis, 22 ga Oktoba, 2020.
Ya ce duk da raguwar rashin kuɗin shiga da ƙasar nan ke fama da shi da kuma tarnaƙin da annobar korona ta ƙaƙaba wa ƙasar, Gwamnatin Tarayya ta fito da tsare-tsare da ke taimaka wa masu ƙananan sana’o’i da matasa da faƙirai ta yadda za a taimaki rayuwar su.
Ya ce, “Gwamnati ta fito da hanyoyi da tsare-tsare na musamman domin matasa da mata da kuma mutane waɗanda ke fama da babu a cikin al’umma. Waɗannan sun haɗa da babban shirin mu na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara nan da shekaru 10. Akwai kuma shirin naira biliyan 75 na Asusun Gina Matasa na Ƙasa inda za a samar da damarmaki ga matasa da kuma ƙanana da tsaka-tsakin sana’o’i, wato asusun ‘Micro, Small and Medium Enterprises (MSME) Survival Fund’, wanda ta hanyar sa gwamnati ke raba lamunin N30,000 ga kowane daga cikin masu sana’a mutum 100,000 tare da ba su tabbacin sayen kayan da su ka yi.
“Sauran tsare-tsaren sun haɗa da ‘Farmermoni’, ‘Tradermoni’, Marketmoni, da shirin ‘N-Power’ da ya ƙunshi ‘N-Tech’ da
‘N-Agro’.
“Babu wata gwamnati da aka yi a Nijeriya wadda a tsanake kuma da gaske ta tunkari matsalar fatara kamar yadda mu ka yi.”
Shugaba Buhari ya yi kira ga matasa da su yi la’akari da kuma su ɗau matakin cin gajiyar waɗannan kyawawan tsare-tsare da wannan gwamnati ta fito da su domin ta kyautata rayuwar su kuma ta hana wasu ɓata-gari su yi amfani da su domin jawo fitina da nufin wargaza shirin dimokiraɗiyyar ƙasar nan.
Ya nanata dagewar gwamnatin sa wajen
inganta rayuwar jama’a da kuma tabbatar da haɗin kan ƙasar nan.