Aisha Buhari ta garzaya da ƴar ta Zahra Buhari ƙasar Dubai inda ta ke sa ran ta haihu a can

0

Aisha Buhari ta garzaya da ƴar ta Zahra Buhari ƙasar Dubai inda ta ke sa ran ta haihu a can

Uwargidan Shugaban Najeriya, A’isha Buhari tana Dubai, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, UAE a halin yanzu tare da tawagarta gabanin haihuwar da ake sa ran ‘yarta, Zahra za ta yi.

Wannan dai ya saɓa da jita-jitar da aka yi ta yaɗawa cewa Uwargidan Shugaban Najeriyar tana Najeriya lokacin da ta bayyana ra’ayinta game da zanga-zangar ƙin jinin Rundunar ‘Yan Sanda ta Musamman Mai Yaƙi da ‘Yan Fashi, wato #EndSARS, wadda matasa suka yi.

A ranar 17 ga Oktoba ne A’isha Buhari ta wallafa wani hoton Shugaba Muhammadu Buhari a inda yake ganawa da shugabannin tsaro, inda ta yi amfani da maudu’in #ACeciJama’a.

Ta wallafa bidiyon ne tare da wata waƙa mai taken Arewa Na Kuka wadda fitaccen jarumin finafinan Hausa, Adam A. Zango ya rera.

Wannan abu da A’isha Buhari ta yi ya sa ‘yan Najeriya da dama sun yi tunanin cewa tana Abuja, Fadar Gwamnatin Najeriya, ta kuma taya ‘yan Najeriya zanga-zanga.

Sai dai binciken jaridar Intanet, SaharaReporters ya gano cewa Uwargidan Shugaban Najeriyar ta shafe kwanaki ba ta Najeriya, kuma ba za ta dawo ba har sai ‘yarta ta haihu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here