AN BA MATA SAMA DUBU BIYU TALLAFI A JAHAR ZAMFARA

0

AN BA MATA SAMA DUBU BIYU TALLAFI A JAHAR ZAMFARA …

Gwamnatin Tarayya ta ba matan karkara 2,800 agajin kuɗi N20,000 kowaccen su a Jihar Zamfara a Shirin Bada Tallafin Kuɗi ga Matan Karkara, wato Grant Project for Rural Women.

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta ƙaddamar da tsarin biyan kuɗin, wanda sau ɗaya ake biya, a Gusau a yau Talata.

A taron, ministar ta bayyana cewa rabon kuɗin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ke yi na cika alƙawarin gwamnatin sa na magance matsalolin rayuwar jama’a.

Ta ce, “An fito da shirin bada tallafin kuɗi ga matan karkara ne (Grant for Rural Women programme) domin a cika alƙawarin gwamnatin Buhari na magance matsalolin al’umma, wanda ya haɗa da muradin ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara da yunwa nan da shekaru 10 masu zuwa.

“An tsara shi domin a samar da hanyar fara bada tallafin kuɗi ga wasu daga cikin matan karkara da su ka fi shan wahala a Nijeriya.

See also  Zaɓen Shugaban Ƙasa: Manyan Dalilan Da Suka Sanya Atiku Abubakar Ya Faɗi Zaɓe

“Za a riƙa bada kuɗi N20,000.00 ga kowace daga cikin matan karkara mabuƙata sama da 150,000 a dukkan jihohi 36 na ƙasar nan da kuma Yankin Birnin Tarayya.

“Ana sa ran tallafin kuɗin zai ba mata dama su samu jarin kuɗi da za su yi sana’o’i. Fatar mu ita ce waɗanda su ka ci moriyar wannan shiri za su yi amfani da wannan damar wajen ƙara hanyoyin samun kuɗin shiga, da ƙara samun abinci da kuma uwa-uba inganta rayuwar su ta yau da kullum.”

Ɗaya daga cikin matan da aka ba tallafin kuɗi N20,000, Malama A’isha, wadda ‘yar shekara 80 ce, ta bayyana jin daɗin ta kan yadda aka yi rabon, kuma ta gode wa Shugaba Buhari saboda ya tuno da matalauta a wannan mawuyacin hali da ake ciki.

Mata 200 daga kowace daga cikin ƙananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara ne za a ba tallafin N20,000 kowaccen su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here