AN SABUNTA KUJERAR SHUGABAN INEC NA KASA MAHMOD YAKUBU

0
190

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙara ba Farfesa Mahmood Yakubu matsayin Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), bayan cikar wa’adin sa na farko.

A cikin wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, Shugaban Ƙasar ya ce ya yi naɗin ne a bisa tanadin Sashe na 154 (1) na Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya, na shekarar 1999 (kamar yadda aka gyara shi).

A wasiƙar, ya faɗa wa majalisar a yau cewa, “Ina farin cikin gabatar da zaɓen Farfesa Mahmood Yakubu, domin amincewar Majalisar Dattijai, don a naɗa shi Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a karo na biyu kuma na ƙarshe.”

Shi dai Farfesa Yakubu, Shugaba Muhammadu Buhari ya soma naɗa shi shugaban hukumar ne a cikin watan Nuwamba na 2015.

A wannan sabon wa’adin ma, zai yi shekara biyar kamar yadda ya yi a na farko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here