MASARI A ‘”‘TSAKA MAI WUYA'””CIKIN KATSINA

0
450

MASARI A ‘”‘TSAKA MAI WUYA'””CIKIN KATSINA

@ Katsina City News

Gaf da Filin Idi na cikin babban birnin Katsina, akwai wata hanyar Ruwa da taso daga nan ta shiga unguwanni guda bakwai, cikin su akwai, ‘Yan Dabinnai, ta ratsa Tudun ‘Yan Dabinnai, ta shiga Turaku, zuwa Lambobi, hanya ce mike har Dan Takum, a tsakanin unguwannin ake kiran yankin ‘Tsaka Mai Wuya’.

Ana kiran yankin ‘Tsaka Mai Wuya’ ne, don kuwa duk shekara in damina ta yi, babu sauran kwanciyar hankali ga sama da gidaje 3,000 da ke yankin da suka ratsa unguwannin.

Unguwanni ne da ake kira na marasa galihu. Ga su cunkushe, ga shi babu wasu manyan ‘yan siyasa ko yan boko da za su iya yi wa halin da suke aciki cara.

Duk damina da an fara ruwa, mazauna unguwannin nan hankalinsu tashe yake. Sama da shekara 10, duk damina sai an yi rusau, wani lokaci har da rasa rai a yankin.

A irin bayanan da Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari yake ji na halin da yankuna marasa gata ke ciki, ya ji labarin yankin da halin da jama’arsa ke ciki.

Gwamnan ya ba da umarni ga Ma’aikatar kula da muhalli ta Jihar Katsina, su kawo bayanin yadda za a fitar da wadannan bayin Allah daga wannan kangin da suke ciki.

Ma’aikatar Muhalli na kammala aikinsu, ya ba da kwangilar yin aikin. Yanzu haka ana aikin magudanar ruwa mafi tsawo da girma da inganci a tarihin Jihar Katsina.akan kudi sama da naira bilyan biyar.

Aikin yana da tsawon kilomita 11, yana da fadin mita 1.2 zuwa 45.ya kumayi ma katsina katanga

An fara aikin a cikin shekarar nan ta 2020, an tsara kammala shi a cikin watan Yuni na 2021 kafin ruwa mai zuwa ya sauka.

Tsakanin gidaje da wurin sana’a da filaye na mutane sama da 250 aikin ya shafa, kuma an biya kusan kashi 80 daga cikinsu kudin diyya.

Akwai ‘yan kadan da suka rage ba a biya su ba, amma ana kan kammala aiki a kansu don a biya su. Diyya kawai an ware sama da Naira miliyan 100.

Mutanen unguwannin sun shaida mana cewa, an rika biyan diyya mai albarka; itace, fili, gida da wajen sana’a, duk wanda aka fada masa me za a biya shi, sai ka ga ya fara tsalle.

Domin aikin ya yi inganci aka dauko wani kwararren kamfani wanda ke da kayan aiki na zamani, shi ne yake aikin. Gwamnan Katsina da kansa akai-akai yake duba aikin don ya tabbatar komai na tafiya kamar yadda aka tsara.

Wannan aiki na magudanar ruwa kwara daya mafi tsawo a tarihin a Jihar Katsina, zai canza rayuwar jama’ar unguwanni guda bakwai, da dubban gidaje, canzawa ta har abada.
Aikin ya samar wa mutane aikin yi sosai, domin kamfanin ya dauko duk ma aikatamsa ne daga jahar katsina.yayin da manyan injiniyoyinsa ke duba aiki.
Mutanen yankin da kansu suke tsare kayan aikin don tabbatar ba abin da ya same su.kuma akai akai su tari leburorin suna masu addu a.
Mun dauko sama da hotuna dari na wannan aikin amma mun zakulo kadan daga cikin su. Mun kuma Dora bidiyon ra ayoyin jama a da muka ji a katsina city TV da sauran shafukan mu.


_______________________________________________
Katsina city news jarida ce dake bisa yanar gizo akan www.katsinacitynews.com da kuma you tube, Facebook da sauran shafukan sada zumunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here