GWAMNATIN TARAYYA TA BAYAR DA HUTUN BIKIN MAULUDI

0

GWAMNATIN TARAYYA TA BAYAR DA HUTUN BIKIN MAULUDI

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Domin taya alummar Musulmai murnar zagayowar ranar Mauludi, gwamnatin tarayya ta bayar da hutun aiki na kwana daya inda ta bayyana ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba, a matsayin ranar hutu domin gudanar da bikin Mauludi (Eid-El-Maulud) da Musulmai ke yi domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad.

Ministan ma’aikatar harkokin ciki gida, Rauf Aregbesola, ne ya sanar da hakan amadadin gwamnatin tarayya, a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mohammed Manga, wanda shi ne daraktan yada labarai da hulda da jama’a a na ma’aikatar harkokin cikin gida, ya fitar,

Sanarwar ta taya murna ga al’ummar Musulmi, inda ta bukaci su yi koyi tare da rungumar kyawawan halaye irin na Annabi Muhammad SAW.

A cewarsa, yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin kasa. Aregbesola ya roki ‘yan Najeriya, musamman Musulmai, da su kaucewa duk wata halayya ta karya doka da tayar da tarzoma a kasa a irin wannan lokaci da wasu batagari ke cigaba da tafka barna.

Ministan ya bayyana cewa Nigeria ce alfaharin duk wani bakin mutum, a saboda haka akwai bukatar ta samu shugabanci da zai tabbatar da cigaban nahiyar Afrika da bakaken mutane.

Kazalika Aregbesola ya bukaci su bawa gwamnatin shugaba Buhari hadin kai a kokarin da take yi na gina musu kasa mai karfi da kowa zai kasance mai alfahari da ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here