IPAC ta taya Yakubu murna kan sake naɗa shi shugaban INEC

0

IPAC ta taya Yakubu murna kan sake naɗa shi shugaban INEC

Cibiyar Shawartar Juna Tsakanin Jam’iyyun Siyasa a Nijeriya (‘Inter-Party Advisory Council, IPAC) ta taya Farfesa Mahmood Yakubu murna kan sake naɗa shi da aka yi a matsayin Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta na mai kira a gare shi da ya ci gaba da yi wa hukumar garambawul kamar yadda ya faro yi a wa’adin sa na farko.

Shugaban IPAC na ƙasa, Dakta Leonard Nzenwa, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya bayar a Abuja a ranar Laraba, inda ya bayyana sake naɗin Yakubu ɗin a matsayin abin da ya dace a yi marhabin da shi kuma albarka ce ga tsarin siyasar Nijeriya.

Nzenwa ya ce a cikin shugabannin da su ka riƙe ragamar hukumar a da, ƙalilan ne su ka samu irin nasarar da Yakubu ya samu a lokacin wa’adin mulkin sa na farko.

Ya ce Farfesa Yakubu ya karɓi ragamar INEC ne watanni huɗu bayan tafiyar Farfesa Attahiru Jega, wanda ya shugabance ta a lokacin muhimmin babban zaɓen shekarar 2015 da ya kawo Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa.

Shugaban na IPAC ya kuma yaba wa Yakubu kan shirin sa na maida komai a kan komfuta wanda hakan ya sauya yadda ake gudanar da zaɓe a Nijeriya a cikin shekaru huɗu da su ka gabata.

Ya ce, “Yadda aka gudanar da zaɓuɓɓukan gwamna a jihohin Edo da Ondo salin alin kyakkyawar alama ce ta ingantacciyar hanyar amfani da fasahar komfuta wadda wa’adin farko na Yakubu ya kawo wa ‘yan Nijeriya.

Nzenwa ya ce, “Mu na kira a gare shi da ya ci gaba da zage damtse domin ya taimaka wajen sauya fasalin tsarin gudanar da zaɓe, kuma mu na kira ga shugaban da ya dage sosai don tabbatar da cewa ƙuri’un ‘yan Nijeriya sun amfanar a dukkan zaɓuɓɓukan da za a yi nan gaba.”

Bugu da ƙari, ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su yi aiki tuƙuru wajen goyon bayan ƙoƙarin sabon naɗaɗɗen shugaban na INEC na ganin duk wani zaɓe a ƙasar nan an yi shi ba tare da wariya ko rashin adalci, kamanta gaskiya ko inganci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here