Wani fursuna da ya gudu a jihar Edo ya kashe wanda ya ba da shaida a kansa a kotu

0

DA ƊUMI-ƊUMI: Wani fursuna da ya gudu a jihar Edo ya kashe wanda ya ba da shaida a kansa a kotu

Ɗaya daga cikin fursunoni 1,193 da suka gudu daga gidajen yarin Oko da Benin na jihar Edo, an sake kamashi da laifin kisan kai.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Babatunde Kokumo ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da wasu mutum 126 da aka kama bisa zargin aikata manyan laifuka, inda ya ce 10 daga cikin su fursunoni ne da suka gudu daga gidan yari a lokacin zanga-zangar EndSars.

Ya ce ɗaya daga cikin su, bayan ya tsere daga gidan yarin Oko, ya wuce zuwa kauyensu a ranar, don ya kashe mutumin da ya tsaya a matsayin shaida a shari’ar da ta kai shi gidan yarin. An kama shi kuma yana cikin wadanda ake tuhuma kamar yadda majiyar Hausa Daily Times ta jaridar The Cables ta ruwaito.

Ya ci gaba da cewa sauran suma da suka tsere daga gidan yarin sun ci gaba da aikata miyagun laifukan da suke yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here