EndSARS: Jihar Legas na nema Tiriliyan daya don sake gina wuraren da aka lalata mata

0

#EndSARS: Jihar Legas na nema Tiriliyan daya don sake gina wuraren da aka lalata mata

Daga Ibrahim Hamisu

Shugaban majalissar Dattawa ta kasa Femi Gbajabiamila, yace Gwamnan Jihar Lagas Babajide Sanwo-Olu yace jihar tana bukatar Naira Tiriliyan Daya domin a sake gina wuraren da masu zanga-zangar #EndSARs suka rusa.

Gbajabiamila ya fadi haka a lokacin da yake hira da yan jaridu a majalissar bayan ziyarar gani da ido kan wuraren da masu zanga zangar suka barnatar a birnin Lagas.

Ya ce majalissar za ta yi duk mai yuwuwa domin biyan diyya ga wadanda rikicin ya rutsa da su, da suka hadar da jami’an yan sanda da suka rasa rayukansu.

Sannan ya bukaci matasa da su kwantar da hankulansu, su kuma bi doka da oda domin dawo da zaman lafiya, tare da bayyana kwarin gwiwarsa kan hadin kan kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here