AN KARAMMA MINISTA SA ADIYYA AKAN AIKIN TALLAFIN KAYAN KORONAVIRUS

0

AN KARAMMA MINISTA SA ADIYYA AKAN AIKIN TALLAFIN KAYAN KORONAVIRUS

Ministar Harkokin Hinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta karɓi wata babbar karramawa ta duniya kan rawar da ta taka wajen aikin agaji lokacin da annobar korona (Covid-19) ta ɓarke a Nijeriya a farkon wannan shekara.

An karrama ministar ne da kyautar da ake kira ‘EuroKnowledge Leadership and Humanitarian Award’ saboda babbar gudunmawar da ta bayar ga jama’a a daidai lokacin da annobar ta yi ƙamari a ƙasar nan.

Kamfanin EuroKnowledge, wanda ya shirya bikin karramawar ta hanyar yanar gizo daga Majalisar Dattawan ƙasar Birtaniya (House of Lords) a ranar Juma’a, ya bayyana jin daɗi tare da yabo ga wasu shugabanni da su ka nuna kyakkyawan misali ta hanyar bada muhimman gudunmawa mai tasiri a sassan rayuwa da su ke aiki a ciki.

A jawabin ta na karɓar kyautar, Hajiya Sadiya Umar Farouq ta gode wa kamfanin Euro-Knowledge, wanda ya na daga cikin nanyan kamfanoni masu bada shawara a duniya, saboda dacewar da ya ga ta yi da wannan karramawa. Ta ce wannan ya zama shaida na ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na tunkara tare da magance matsalolin da cutar korona ta haifar ga ‘yan Nijeriya.

Ta ce: “Ina so in bayyana godiya ta ga EuroKnowledge saboda zaɓa ta da su ka yi, su ka ba ni wannan kyauta mai suna ‘Best National Humanitarian Response to COVID-19 Crisis Award’ a Majalisar Dattawa da ke London. Na gode da ku ka lura da aikin da mu ke yi wa al’umma.”

Ministar ta ce aikin da ake yi yanzu na agajin jama’a, farawa ne ma na abin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta shirya a burin ta na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara da yunwa nan da shekara goma masu zuwa.

See also  CONSTRUCTION OF THE NATIONAL DIGITAL INNOVATION AND ENTREPRENEURSHIP CENTRE IS ON COURSE!

Ta ce, “Wannan karramawa ba wai tawa ce ni kaɗai ba, a’a har ma da Gwamnatin Tarayya da Jihohi da Ƙananan Hukumomi da ma mutane da hukumomi da ke Nijeriya waɗanda ke aiki tuƙuru domin su agaji milyoyin ‘yan Nijeriya waɗanda annobar korona ta shafi samun kuɗin su.

“Ina so in bayyana sadaukarwar Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da Shugaba Muhammadu Buhari wanda shi ne ya kafa Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa. Aikin wannan ma’aikata shi ne samar da nagartacciyar hanyar da za a gudanar da ayyukan jinƙai na ƙasa da na duniya don tabbatar da cewa an rage tare da shirya wa faruwar bala’i, da gudanar da ayyukan taimakon jama’a a Nijeriya. Kuma na sadaukar da wannan karramawa ga abokan aiki na.”

Hajiya Sadiya ta ce wannan karramawa ta ba ta ƙwarin gwiwa domin ta ƙara ƙaimi bakin iyawar ta wajen yi wa ‘yan Nijeriya aiki.

Wasu waɗanda su ma an ba su irin wannan kyautar karramawar sun haɗa da Sallo Polak (Babban Darakta na Philanthropy Connections a ƙasar Thailand), da Mai Girma Ernest Koroma (tsohon Shugaban Ƙasar Saliyo), da Mista Christian Paradis (tsohon Ministan Ciniki da Masana’antu na ƙasar Kanada), da Benedict Lee (sabon shugaban Kulob ɗin Rotary a ƙasar Hong Kong), da Mista Tsvi Gal (tsohon shugaban bankin Morgan Stanley da ke Amurka), da Dakta Manu Chandaria (wani biloniya a ƙasar Kenya kuma shugaban kamfanonin Comcraft Group, Kenya)

Wasu ‘yan Nijeriya da su ma aka karrama su sun haɗa da Dakta Mahmood Ahmadu (Shugaban kamfanin Integrated Online Services), da Miss Florence Otedola (shugabar cibiyar DJ CUPPY Foundation), da kuma Dakta Anthony Nwachukwu (shugaban kamfanin Innovate Pay 1).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here