Kwana 360 A Ofishin KASROMA: Injiniya Suraj Yazid Dadin Kida Ka Sanya Kirari
Daga El-Zahardeen Umar, Katsina
Tafiyar da shugabanci wata kyauta ce da kuma baiwa da Allah ta’ala ke yiwa bawa domin sanin abinda ke cikin zuciyarsa wannan ko shakka babu muna iya ganin haka a daidai lokacin da hukumar kula da gyaran hanyoyi da fitilu ta KASROMA ke cika shekara guda da samun shugabacin injiniya Suraj Yazid.
Matsaya ko mataki da shugaba ke dauka a dukkanin al’amura shi ne ke zama jagora wajan aiwatar da abin kirki ga jama’a ko akasin haka, domin saboda su ne ya ke shugabantar wannan hukumar, ita ma KASROMA na daga cikin sahun farko da ta da ce shugaban a wannan gwamnati ta Aminu Bello Masari.
Abubuwan da jama’a suka amfana da shi a karkashin jagorancin Injiya Suraj Yazid Abukur abu ne da ya kamata ya shiga kudin tarihin wannan jiha, domin wadanda suka amfana da aikin wannan hukuma sun fada da bakin su cewa wannan karon ne na farko da suka ji sunan wannan hukuma sannan suka ganta ido-da-ido a garuruwan su domin aiwatar da ayyukan cigaban kasa.
Ita wannan hukuma ta gyaran hanyoyi da fitilun kan titi wannan ne karon farko da ta da ce da miji irin ta wato dai kamar yadda bahaushe ke cewa kowace kwarya da abokin burminta, sai yanzu ta tabbatar ta auri miji wanda zai kare hakkinta da kuma mutuncinta.
Zaben Injiniya Suraj Yazid Abukur da aka yi a matsayin shugaban wannan hukuma kai kasan ba karamin tunani da hangen nesa aka yi ba, saboda abubuwan da ke faruwa kafin zuwansa wannan hukuma da kuma yanzu da ya zo, sun I shi mai hankali gane abinda nake nufi da cewa sai yanzu ne KASROMA ta yi miji na gari.
Tun asali daman wannan hukumar tana bukatar mutun wanda yake da ilimi da kwarewa tare da samun lasisi daga kungiyoyin kwararu na injiniyoyi domin ta haka ne kawai za a yi abinda ya da ce a wannan hukuma, amma dai kuskuran da aka yi a baya yanzu ake ganinsa ya fito fili.
Sannan kalubalan da wannan hukuma take fuskanta na kasancewarta a hannun mazajen da aka yi mata auran dole da su, sai yanzu ne za a yi baban gyara domin samun damar dora harsashen cigabanta ta yadda za ta da ce da dokar da ta kafa ta a hukumance.
Babu wani mutun a jihar Katsna da yake da shakku game da aikin da wannan hukuma take yi, yanzu maganar da ake wannan hukuma ta yi tsarin da kowace karamar hukuma za a amfana da wannan hukuma kuma an fara gani a kasa ba labari ba.
Salo da tsarin da Injiniya Suraj Yazid Abukur ya dauka bayan kama aikinsa a ranar 13 ga wata Oktoba na shekarara 2019 abi ne da ya kamata masu mulki su yi koyi da shi domin dai ko ba komi ya zo da sabbin tsare-tsare da suka taimaka wajan bunkasar wannan hukuma kamar yadda zamu gani anan gaba.
Wani abin birgewa game da Injiniya Suraj Yazid Abukur shi ne lokacin da ya fara aiki, ya zauna tare da tattaunawa da duk wani mai ruwa da tsaki da zai iya bada tasa gudunmawa domin a samu nasarar da ake bukata a wannan hukuma.
Mun ga yadda ya rika kai ziyarorin ban girma da neman shawara, domin akwai wata maganar hikima da ke cewa “babu abinda ya kai shawara daidaita al’amura, muna iya gann haka daga wannan bayan Allah.
Kai ziyarori a hukumomi irin na ‘yan Sanda da hukamar kiyaye hadura ta kasa da bangaran kungiyar direbobi da kungiyoyin al’umma domin jin abinda ya dame su sannan ya san yadda zai tsara ayyukan da za su amfane su, hakika hakan ya taimaka masa matuka gayya wajan samun nasara da ake gani yanzu haka.
Shin wai daman akwai wannan hukuma? Wannan ita ce tambayar da wasu da suka rika yi a lokacin da aka je yi masu aikin domin bunkatarsu wanda kuma sun kai kuka har sun gaji amma babu amo ba labari, kwatsam sai ga sabon shugaban wannan hukuma Injiniya Suraj Yazid Abukur ya shi go gari-gari domin share hawayen jama’a, madalla da wannan kokari naka.
Tuntuba da dogon tunani da shugaban wannan hukuma ya yi a lokacin da ya fara aiki abu na kwararu domin ba kowa bane ke wannan tunani balanta har ya kai ga nasara, a jawabin da ya yi na cika shekara guda akan karagar mulkin wannan hukuma, Injiniya Suraj Yazid Abukur ya fada da bakinsa cewa shawarwari sun taimaka matuka gayya wajan samun wannan nasara tasa da ake kwatantawan da ta shekara goma da suka wuce.
Zaku yarda da ni cewa sai yanzu ne KASROMA ta yi miji na kwarai domin kamar yadda na ambata cewa wannan hukuma Allah ya albarkaceta da kayan aiki da suka hada da manyan motoci na zamani da kayan aiki wanda hakan ke kara nuna cewa gwamnatin Aminu Bello Masari ta shirya kuma ta ba wannan hukuma damar ta yi aikin ta kamar yadda doka ta tsara.
Motocin da kayan aikin da ake da su kafin zuwan Injiniya Suraj Yazid Abukur sai da ya tabbatar da cewa wadanda suka lalace ko suka daina aiki an gyara su kuma wadanda ake bukata babu an kawo su, domin ya fada cewa kayan aikin na taimakawa kudirin shugaba na samun nasara a kowace irin ma’aikata.
Kamar yadda na fada a baya, bayan ya gyara abubuwan da ya taras a wannan hukuma,duk wani abu da za agani yanzu ya samu ne sakamakon sabon tunani Injiniya Suraj Yazid Abukur wanda na tabbatar ko jama’a shaida ne akan haka.
Bari mu duba wasu ayyuka da muka gani anyi a karkashin jagorancin Injiniya Suraj Yazid Abukur kafin mu kai ga duba wandanda ya tsara zai gudanar idan Allah Ya ba shi iko yin hakan, domin komi sai Allah Ya yarda.
A wannan shekarar ta 2020 akwai sabon tsarin da wannan hukuma ta zo da shi kamar yadda gwamna Aminu Belo Masari ya ba su dama na yin ayyukan ga jama’a wanda dama domin su ne aka kafa wannan hukuma kuma aka aura mata miji na gari don ta haifar da da mai ido, gashi kuwa abinda muke gani yanzu ya tabbata.
An tsara cewa a wannan shekarar kawai kananan hukumami 6 za su amfana da hanyoyi a cikin shalkwatar karamar hukumar kuma an zabi biyu daga kowace shiyya inda a Katsna an zabi Batsari da Kaita sai a Funtuwa a zabi Kafur da Dandume a ya yin da yankin Daura aka zabi Mai’adua da kuma Kusada.
Sannan akwai tsari na cigaba da wannan aiki a shekarara 2021 inda za a sake zabar wasu kananan hukumomi guda shida domin cigaba da aikin. Wannan ana maganar shinfida tituna ba wai gyaran hanya ba, idan muka dauko maganar gyaran hanya ka wai lokaci ba zai bari mu fadi abinda Injiniya Suraj Yazid Abukur ya yi ba a cikin shekara guda da zuwansa wannan hukuma.
Haka ma akan maganar gyara da kuma sanya sabbin fitillun kan tituna da gyara su shima wani babin ne na musamman, amma duk da haka muna cewa Injiniya Suraj Yazid Abukur mun gani a kasa ba labari ba. Kuma muna nan muna zuba idonu a cikin shekarar 2021 idan Allah Ya kaimu da rai da lafiya.
Haka kuma wannan hukuma ta KASROMA muna cigaba da yi mata fatan alheri da addu’o’in samun nasara ta dore daga abinda muke gani na kamun ludayin aikinka. Sannan shi kanshi mai girma gwamna muna da kwakwawan fatan cewa zai kara baka dama akan wanda yake baka, domin samun nasarar gwamnatinsa a wannan bangare baki daya.