YAN BINDIGA SUNKAI HARI KAUYEN SHIRGI.

0

YAN BINDIGA SUNKAI HARI KAUYEN SHIRGI.
Aliyu mustafa
@ katsina city news

Da misalin karfe tara na daren (9:00pm) asabar 31-10-2020 wasu ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Shirgi dake cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
‘Yan bindiga da aka labarta mana adadin su bai wuce shidda ba, biyu daga cikinsu, biyu kadai ke dauke da bindiga.
sun harbi wani matashi mai suna Sha’aibu Dadin kowa dake kan hanyar sa ta komawa gida daga Shirgi da yake a ranar ne kasuwar Shirgi ke ci. Kuma kauyukan suna kusa da juna, sannan sun bindige wani mazaunin Shirgi mai suna Basiru Gwanki, dake gudun ceton rai amma yayi taho mu gama da harsashin su.ya riga mu gidan gaskiya. Tuni akayi jana’izar su da safiyar lahadi.
‘Yan bindigar sun kutsa kai gidan wani Alhaji Gambo suka kwance shanun sa guda biyu.
Daga nan sun sake shiga wani gida, koda yake dai bamu iya tantance mai gidan ba. Sannan sun fada kauyen Kururuwa inda suka kore masu garke awaki suka rankaya dashi da kuma shanun da suka sato Shirgi.
Da dai lamarin hare-haren a yankunan Batsari ya lafa, amma kwatsam sai aka ji bullar su wannan kauye dalili kenan da yasa jama’a ke ta dar-dar da jin wannan harin na Shirgi.
________________________________________________
Ziyarci shafukan jaridun www.katsinacitynews.com da www.taskarlabarai.com da kuma www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta na shafukan. Duk sakon Kira ko tes aiko ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here