YAN DABA SUN KASHE MATASHI A KANO

0

MAULIDI: ‘YAN DABA SUN KASHE MATASHI A KANO

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Wasu gungun ‘yan daba a unguwar Sani Mainagge da ke cikin birnin Kano a karamar hukumar Gwale sun kashe wani matashi mai suna Auwalu Halilu a yunkurinsu na yi masa kwace bayan ya taso daga mauludi.

Kano Focus ta ruwaito al’amarin ya faru ne a daren ranar Lahadi ya yin da ake tsaka da yin Mauludi a yankin.

shaidun gani da ido sun ce ‘yandaban na fakewa ne a cikin makabartar Gwale su kuma tare dukkanin wanda ya taso daga wurin mauludi ko kuma zai wuce ya tafi harkarsa su yi masa kwace.

A cewar Muhammad Shehu ‘yan daban sun tare Auwalu Halilu ne cikin dare da nufin yi masa kwace, suka kuma soke shi da hakan ya yi sanadiyyar ransa.

Ya ce tun da aka fara mauludi ‘yan daban ke fakewa cikin taron masu mauludin sun aikata ta’asarsu.

Malam Shehu ya ce ‘yan daban sun mamaye unguwar ne ta Sani Mainagge a daren Lahadin da misalin karfe biyu na dare har zuwa karfe uku suna cin karensu ba babbaka.

Ya ce ya samu tsagewar kashi sakamakon saran da ‘yan daban sukayi masa.

Sa’idu Ahmad dan uwa ne ga marigayin, ya ce ayyukan ‘yan daban ya dade yana addabarsu a unguwar, a cewarsa wani lokacin ma har gidajen jama’a suke shiga.

“Munyi iya yin mu amma abin yaci tura muna kira da a dauki mataki.

Anata bagaren mahaifiyar mamacin, Naja’atu Musa Sheka tayi kira ga mahukunta dasu kwato mata hakkin danta.

a cewarta ko kadan su ‘danta bai aikata laifin komai ba amma an rabashi da duniya.

Ta kara da cewa bayan da aka sari ‘dan nata sun sanar da hukumar ‘yan sanda.

“Muna da yara da yawa ya kamata mahukunta su kawo karshen wannan al’amari.

A cewar ta za su zuba idanu su ga hukuncin da jami’an tsaro za su dauka wajen nemo hakkin danta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here