YAN SANDA A KANO SUN KAMA MAI SAYAR DA TAKARDUN DAUKAR AIKI NA BOGI
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Rundunar ‘yan sanda jihar Kano ta sami nasarar kama wani mutum mai suna Rabi’u Sani mazaunin karamar hukumar Dala mai shekaru sittin da biyu yana siyar da takardar daukar aiki ta bogi.
DSP Abdullahi Haruna Kiyawa mai magana da yawun rundunar yansada ta jihar Kano ne ya tabbatar da kama mutumin.
Wanda ya ce sun sami korafi ne daga wata mata da ya karbi kudinta ya bata takardar daukan aikin ta bogi.
Kuma ba suyi kasa a gwiwa ba suka tsananta bincike tare da kamo shi.
Kiyawa ya kara da cewar bayan kamoshi ya tabbatar da cewar sana’arsa ce buga takardun daukar aikin na bogi suna siyarwa da mutane.
Kuma sun buga takardar guda talatin tare da karbar kudi kimanin miliyan uku da dubu dari takwas a hannun mutane .
Haka kuma rundunar ‘yan sanda ta kamashi da wasu takardun daukar aikin wanda zai siyar a nan gaba da kuma tsabar kudi miliyan daya da dubu dari biyu.
Mutumin da ake zarginsa da siyarwa da mutane takardun daukar aiki na bogi Rabi’u Sani ya ce su uku suke gudanar da sana’ar tasu ta siyar da takardun bogin.
Ya ce masu neman aiki a Ma’aikatar ilimi suke siyarwa da takardar daukan aikin wanda suke karbar kudi a hannunsu daga dubu arba’in zuwa sittin domin siyan takardar daukan aiki.