Zanga-zanga Ta Ɓarke A Amurka Sakamakon Zaɓen Shugaban Ƙasa

0

YANZU-YANZU | Zanga-zanga Ta Ɓarke A Amurka Sakamakon Zaɓen Shugaban Ƙasa

Zanga-zanga ta ɓarke a wasu biranen Amurka yayin da ake dakon sanin wanda ya lashe zaben shugaban ƙasa.

Zanga-zangar ta kasu kashi biyu, da waɗanda ke son a cigaba da ƙirga ƙuri’a da kuma waɗanda ke son a dakatar, a daina, a kuma bayyana wanda ya samu nasara a haka.

Dandazon mutane sun taru a titunan wasu daga cikin jihohin ƙasar kamar New York da Washington da Pennsylvania suna neman a cigaba da ƙirga ƙuri’un da suka rage.

Wasu kuwa sun taru a cibiyar ƙidaya ƙuri’u dake jihar Michigan, in da aka bayyana Biden a matsayin wanda ya lashe jihar.

Da alama masu son a cigaba da ƙirga ƙuri’a magoya bayan Joe Biden ne, yayin da magoya bayan Trump ke cewa a daina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here