APC a zamfara ta yaba wa kwamitin Buni saboda sake dike marakar jam’iyyar a kasannan

0

APC a zamfara ta yaba wa kwamitin Buni saboda sake dike marakar jam’iyyar a kasannan

Daga Shuaibu Ibrahim Gusau

Jam’iyyar( APC) All Progressive Congress reshen jihar Zamfara , karkashin jagorancin , Alhaji lawal liman ta yabawa kwamitin riko na kasa na jam’iyyar karkashin jagorancin Gwamna MaiMala Buni na jihar Yobe saboda kokarin da ta yi na sake kafa jam’iyyar.

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar, Alhaji Lawal Liman ya yi wannan yabon ne a lojacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Gusau , yayin da yake tsokaci kan shirin jam’iyyar na yin rajistar mambobin ta a duk fadin kasar.

Liman ya kara da cewa kwamitin da Buni ya jagoranta ya cancanci yabo saboda ya yi nasarar warware rikice-rikicen da ke faruwa a jam’iyyar a jihohi da dama a kasannan .

Ya ce “Shirye-shiryen kwamitin Buni don magance matsalolin jam’iyyar sun fara bayar da kyakkyawan sakamako a Jam’iyyar .

Liman ya ce“A madadin dukkan mambobin jam’iyyar APC a jihar zamfara, muna goyon bayan matakin da kwamitin Buni ya jagoranta na ciyar da jam’iyyar gaba a halin yanzu.

See also  JAM IYYAR APC TA DAKATAR DA SABO MUSA

Kuma “Ina kira ga mambobin APC musamman a jihar Zamfara da su goyi bayan shugabancin APC na yanzu wajen sake sanya jam’iyyar zuwa wani kyakkyawan matsayi”, in ji Liman.

Ya gargadi mambobin jam’iyyar a jihar kan adawa da jam’iyyar, yana mai cewa jam’iyyar ba za ta lamunci irin wadannan ayyukan ba.

Ya yi kira ga mambobin jam’iyyar APC a jihar da su rungumi zaman lafiya da hadin kai domin jam’iyyar ta ci gaba da karfinta a jihar.

Ya ce”Ku na sane cewa taron jam’iyyar na NEC na watannin baya karkashin jagorancin Shugaba Muhammad Buhari ya yanke shawarar cewa ya kamata a janye kararrakin mambobin jam’iyyar da ke gaban kotu game da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jam’iyyar”, Liman

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here