TARIHI DA DALILAN YIN BIKIN TAKUTAHA A KANO

0

TARIHI DA DALILAN YIN BIKIN TAKUTAHA A KANO

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Shekaru kusan dubu da suka gabata, Kano ba gari bane, Shirayi ne kawai, kamar yadda marubucin wakar Bagauda ta Kano ya bayyana.

Bayan ya zama gari, sai da aka shafe shekaru 100 ana zaune babu addini sai maguzanci a kusa da dutsen Dala.

Acikin watan dai, rundunar musulmi suka fuskanci, rundunar maguzawa, a gefen Dutsen Dala, inda suka hadu, aka gwabza.

A wannan lokacin ne, Jarmai Bajere ya samu nasarar kutsa kai cikin shigifar Tsumburbura, inda ya samu wani halitta na tsaye, rike da maciji a hannunsa, ya daga mashi ya bugawa halittar nan, tayi kuwwa ta fito a guje.

Nan da nan suka bita, inda ta nufi kofar ruwa, ta fada cikin ruwan Dankwai.

Wannan Shi ya kawo karshen Tsumburbura, da kuma addinin maguzawa a garin Kano

See also  SIRRIN MAGANIN CIWON KODA (KIDNEY PAIN)

samuwar wannan Nasara, ba karamin abu bane a wurin musulman Kano.

Wanda aka shafe sama da shekaru 100 ana nema.

A dalilin haka ne, ya sanya musulman kanawa duk shekara, sukan taru su hau Dutsen Dala domin tunawa da wannan nasara da musulunci yayi akan Maguzanci.

Su nunawa duniya cewa, addinin Allah yau ya shafe addinin kafirai.

Domin kafin zuwan musulunci, ba mai hawa Dala in ba Babban limamin addinin ba.

Amma zuwan musulunci, yanzu kowa ma sai ya hau, ya yi kashi ma akai.

Wannan shi ne dalilin da ya sanya ake takutaha a duk shekara a Kano. amma wasu da basu san tarihin ba, ke ganin jahilci ne, ko kuma abu ne, da ya sabawa addinin musulunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here