An bayyana rasuwan malami Aliyu ‘yandoto a matsayin babban rashi ga al’umar jihar Zamfara—- Sani gwamna
Daga Shu’aibu Ibrahim gusau
Mataimakin Shugaban Jam’iyya na shiyyar Zamfara ta Tsakiya, Alh Sani Gwamna Mayanchi ya bayyana rasuwar Shugaban Hukumar Kula da Kananan Hukumomin ta Zamfara Malami Aliyu Yandoto a matsayin babban rashi ga daukacin al’ummar jihar.
Alh Sani Gwamna wanda ya bayyana hakan ta hanyar sakon ta’aziya da aka aike wa manema labarai a Gusau a ranar Lahadi ya ce, shi da dukkan mutanen Zamfara ta tsakiya za su yi kewar marigayi dan siyasa saboda tawali’u da jajircewarsa na siyasa don ci gaban jihar ta Zamfara.
Ya ci gaba da bayyana marigayi Malami Yandoto a matsayin mutum mai tawali’u kuma jajirtacce wanda ya yi imani da kyawawan manufofin da ci gaban jihar ta Zamfara yana mai bayanin cewa zafin mutuwarsa zai ci gaba da kasancewa cikin tunanin dimbin mutanen jihar masu son ci gaban jihar.
Ya kara da cewa” A matsayina na aboki kuma aboki na siyasa ni da Marigayi Malami Yandoto muna musayar ra’ayoyi daban-daban na siyasa musamman lokacin da muke jam’iyya guda ta ANPP da kuma daga baya APC kuma a matsayin wanda ya fito daga yankin Sanatan Zamfara ta Tsakiya irin gudummawar siyasarsa da ra’ayinsa koyaushe yana bayyana a cikin canjin.
Ya ce “A madadin mutanen Zamfara ta Tsakiya musamman magoya bayan jam’iyar APC( All Progressive Congress) muna ta’aziyya ga gwamnati da jam’iyyar PDP mai mulki bisa rasuwar dan jam’iyarsu ma’aikaci kuma jajirtatce, Malami Aliyu Yandoto”.
“Muna kuma yin ta’aziya ga danginsa da kuma mutanen Masarautar Tsafe a kan wannan babban rashi kuma muna addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya sanyashi aljannar firdausi madawwamiya” inji shi Sani Gwamna .