BA MU JIKKATA BA: ALLAH YA JIKAN DIREBANMU!

0

BA MU JIKKATA BA: ALLAH YA JIKAN DIREBANMU!

Alhamdullilahi, Muna godiya da kiraye-kirayen wayarku, hakika ban so cewa ko Kala akan wannan Abu da ya faru da tawagarmu ba, amma rubuce-rubucen jajenku a wannan kafar. Da Kiran wasu da dama da ba mu samu damar daga wayarku ba, saboda cinkoson Kiran.

Allah jikan direbanmu da Allah ya yi wa cikawa. Mu kuma da mu ka rage a Raye Allah ya sa mu cika da Imani.

Albishin da na ke yiwa kowa shi ne. Dukkaninmu babu wanda ko kwarzane ya yi. Duk wanda ya ganni a cikin garin Gusau yau zai tabbatar da haka!.

Haka duk wanda ke cikin wannan tawaga ta mu a yau dole ya gogewa Allah, tare da jinjina ga jajirtattun jami’an tsaronmu musamman na Soji da kullum ba su yin kwana. Dan mu, mu yi.

Allah duk wani Wanda ke kyamar Kasarmu da jaharmu su zauna lafiya allah kadda ka bar shi ya zauna lafiya

Abdulmalik Saidu Maibiredi
9-11-2020

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here