Jam’iyyar Apc Reshen Jahar Zamfara Ta Kori Sen Kabiru Marafa.
Shugaban Jam’iyyar Apc na Jahar Zamfara Hon Lawal M Liman Gabdon Kaura Ya Bayyana Cewa A Hukuman ce Dama Jam’iyyar Apc Reshen Jahar Zamfara ta Dakatar Da Kabiru Marafa Tun Shekarar 2019, Saboda Wasu Laifukka daya Aikata da Suka Sabama Kudin Tsarin Jam’iyyar ta Apc.
Shugaban Na Jam’iyyar Apc na Jaha Ya Bayyana Haka ne Alokacin dayake Mayar da Martani akan Bakaken Maganganu da Kabiru Marafa Yayi Ga Shuwagabannin Riko na Jam’iyyar Apc ta Kasa.
Hon M Liman Gabdon Kaura Ya bayyana Cewa A Shekarar 2019 Jam’iyyar Apc Reshen Jahar Zamfara, ta Gabatar da Takardar Dakatar da Sen Kabiru Mafara ga Uwar Jam’iyyar Apc ta Kasa Lokacin Kurarren Shugaban Jam’iyyar ta Comrd Adams Oshomole, amma Saboda Wasu Biyan Bukatu da Suke Samu Daga Kabiru Marafa na Ganin Sun Ruguza Jam’iyyar Apc a Jahar Zamfara Yasa Suka Ki Fitar da Takardar Korar ta Kabiru Marafa.
“Muna Kira Ga Shuwagabannin Riko na Jam’iyyar Apc ta kasa Dasu Sanyama Takardar Hannu akan Korar Kabiru Marafa daga Jam’iyyar, Bamu Kallon kabiru Marafa a Matsayin Dan Jam’iyyar Apc saboda Jam’iyyar PDP Tana Amfani dashi Domin Ganin Ta Kara Kawo Rikici acikin Jam’iyyar ta Apc”
Dan Haka Muna Kara Kira ga Sauran Ya’yan Jam’iyyar Apc na Jaha dasu daina Kallon Kabiru Marafa Matsayin Dan Jam’iyyar Apc.
Rashin Biyayya ga Umurnin Shugaba Buhari da Shuwagabannin Riko na Jam’iyyar Apc ta Kasa Shikadai Ya Isa Ya zama Dalilin Nuna Cewa Kabiru Marafa Bayama Jam’iyyar Apc Fatan Alhairi.
Daga Karshe Muna Kira Ga Shuwagabannin Riko na Jam’iyyar Apc ta Kasa Su Dauki Kwakwaran Mataki akan Kabiru Marafa, Bisa Fadin Bakaken Maganganu da Yayi Gare su.
Haka Kuma Hon Lawal M Liman Ya Jinjinama Shuwagabannin Riko na jam’iyyar Karkashin Jagorancin Maimala Buni’s Akan irin Na Mijin Kokarin Su Wajen Ganin Sun Hada kan Yayan Jam’iyyar Waje Daya.
*Sanya hannu:-*
*Hon Lawal M liman*
*State Apc Chairman*