Tsarin tattaunawa da ‘yanbindiga yanada amfani— Matawalle
Daga Shuaibu Ibrahim Gusau
Gwamna Bello Mohammed (Matawallen Maradun) ya ce tattaunawa tare da ‘yan fashi yana da amfani sakamakon ta hanyar tattaunawar aka samu nasarar sako ‘yan mata 26 ‘yan asalin jihar Katsina, dukkansu yara kanana, wadanda ‘ yan ta’addan suka dauka aka kuma karbosu ba tare da biyan kudin fansa ba.
Bello ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar yaran bayan an sakosu, ya kara da cewa ‘Yan matan da’ yan fashi suka sace a karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina an kawo su cikin dajin jihar ta Zamfara amma gwamnatin ta gano su, kuma an sake su ta hanyar tattaunawar da aka yi a karkashin yarjejeniyar shirin zaman lafiya.
Gwamnan Matawalle wanda ya amshi ‘yan matan da aka kubutar, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi watsi da tattaunawar sulhu da’ yan bindiga ba saboda ta hanyar bude wuta kadai ba za ta iya magance matsalar ‘yan ta’adda a jihar ba.
Ya ce, “Wannan shaida ce ga hangen nesanmu na tsunduma‘ yan fashi a tattaunawar zaman lafiya. Ga wadanda suka yi imanin cewa ba daidai ba ne mu tattauna da ‘yan fashin, kubutarda wadannan kananan yara wadanda suke’ yan mata ne, ba tare da wani rauni ba, hakika ba karamin aiki bane.
Matan 26 da aka ceto, waɗanda shekarunsu suka kai tsakanin 8 zuwa 12 an duba lafiyarsu kuma an basu sabbin tufafi.
Gwamna Matawalle ya ba da umarnin dawowar su jihar Katsina lami lafiya, lamarin da ya kawo adadin wadanda ‘yan bindiga suka sako a makon da ya gabata zuwa sama da 40.
A halin da ake ciki, Matawalle ya bayyana matakin fatattakar duk wani mutum ko wata kungiya daga ciki da wajen jihar da aka samu ko suna tallafawa ko taimakawa, ko kuma jagorantar ‘yan fashi a jihar.