Mutane miliyan daya zasu ci gajiyar shirin Matawalle N-PASS
Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Gwamnan jihar Zamfara Hon. Bello Mohammed ya bullo da shirin rage radadin talauci na (N-PASS) ga talakawa mutane miliyan daya a jihar zamfara.
Ya bayyana hakan ne a wata takarda mai dauke da hannun Darakta Janar na yada labarai na gidan Gwamnati , Yusuf idris Wanda aka raba wa manema labarai a yau.
Ya ce N-PASS shiri ne na Majalisar Dinkin Duniya, inda masu cin gajiyar za su karbi N5,000 a cikin asusun ajiyar su na banki domin bunkasa kananan kasuwancin su. .
A lokacin kaddamarwar, Gwamna Bello Matawalle ya ce ya bullo da wasu tsare-tsare domin karfafawa wasu daga cikinsu gwiwa, wadanda ofishin matar tasa ke gudanar da su a Zamfara tun bayan hawansa mulki a bara.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta fahimci mahimmancin yaki da talauci da inganta tattalin arziki don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’ummominmu, wanda ke karkashin kulawar Hukumar Bunkasa Tattalin Arziki ta Jihar Zamfara (ZASSIP), wanda a karkashinta mutane 8,692 suka fito Daga kowace Kananan hukumomi 14, ana biyan N10,000 duk wata, sannan N50,000 duk wata ana biyan masu kula dasu a Kananan Hukumomin.
A cewarsa, a daya bangaren kuma, ana aiwatar da shirin na tallafawa mata na musamman a karkashin Ofishin Uwargidan Shugaban kasa, ta inda mata 1,800 daga kananan hukumomi 14 suka samu N20,000 kowannensu.
Ya kara da cewa an gano wadanda suka ci gajiyar shirin a matsayin wadanda ‘yan ta’addan suka addaba yayin da za a biya wadanda suka ci gajiyar shirin a dukkan kananan hukumomin 14 na tsawon lokaci har zuwa wani lokaci. wanda ke haifar da kirkirar rukunin gidaje miliyan daya tare da adadin mutane 2,000 a kowane wata shida.