Yan bindiga sun sace hakimin garin matseri sun kashe mutun daya

0

‘Yan bindiga sun sace hakimin garin matseri sun kashe mutun daya

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Duk da kokarin da gwamnatin jihar zamfara takeyi na kawo karshen ‘yan ta’adda da suka addabi jihar, a Daren jiya jama’ar grain Matseri dake karamar hukumar Anka sun kwana cikin tashin hankali da jimami .

Sakamakon shigowan da ‘yan ta’adda sukayi cikin dare a kauyen har ‘Yan bindigan sun sace Hakimin kauyen, Alhaji Halilu Tudun Matseri tare da yaransa hudu.

Barayin sun kuma kashe wani mutum mai suna Malam Maigaiya Matseri wanda ke kan aikin ceto,

Da yake tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da danjarida , Sarkin Anka, wanda kuma shi ne Shugaban majalisar sarakunan jihar ta Zamfara, Alhaji Attahiru Ahmed.

Ya ce maharan sun je garin ne da sanyin safiyar yau inda suka yi awon gaba da hakimin da yaransa.

Sarkin ya yi addu’ar Allah ya dawo da hakimin da aka sace tare da yaransa, tare da yin kira ga jami’an tsaro da su rubanya kokarinsu na yaki da ‘yan bindiga a jihar.

Wani dan asalin garin, Malam Mohammed Musa ya fada wa wakilinmu cewa, ‘yan bindigar da suka zo garin a kan babura da misalin karfe 2 na daren yau ba su taba kowa ba sai hakimin da ‘ya’yansa.

“Sun zo ne a kan babura suka tafi kai tsaye gidan hakimin inda suka yi awon gaba da shi da yaransa hudu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here