An bukaci matawalle ya taimaka ya biya Daily trust da wasu bashin da suke bin gwamnatin zamfara

0
303

An bukaci matawalle ya taimaka ya biya Daily trust da wasu bashin da suke bin gwamnatin zamfara— Abdulfatai Abdulsalami

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Manajan ayyuka na musamman na jaridar Daily Trust mai kula da jihohin Kebbi da Sakkwato da Zamfara, Abdulfatai Abdussalami, ya roki Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara da ya biya sama da Naira miliyan 8 ga wasu jaridun kasar ciki har da Daily Trust kasancewar wani bangare na bashin da aka gada daga gwamnatin da ta gabata.

Abdussalami, wanda ya bayyana hakan a wata zantawa da ya yi da manema labarai a sakatariyar kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya (NUJ) Gusau babban birnin jihar ta Zamfara.

Ya ce tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari ta sanyasu aiki a lokuta da dama don tallata wasu aiyuka na jihar zamfara.

Ya kara da cewa, izinin fara buga aiyukan na gwamnatin jihar Zamfara ta lokacin , ya fara ne daga shekarar 2018 ta hannun tsohon Mai Baiwa Gwamna shawara na musamman kan aiyukan wayar da kan jama’a da yada labarai da sadarwa, mal Ibrahim Magaji Dosara.

Jaridun da abin ya shafa baya ga jaridar Daily trust sun hada da, Leadership da Blueprint da The Authority da kuma The Guardian da sauran su wanda har zuwa yanzu suna kan gwagwarmayar tabbatar da biyan.

Ya ce”Na ga ya zama dole mu gudanar da wannan taron manema labarai kasancewa ita ce hanya da kawai zamubi don sanar da Gwamna Bello Muhammad mai ci bukatunmu na biyan kudaden da aka bayyana ana gadon su daga gwamnatin da ta gaba.

“Na fahimci cewa bisa wasu tsare tsaren da suka tsara hakan ta yadda za a iya ganin Gwamna Matawalle don Sanar dashi mawuyacin halin da muke ciki, saboda yadda kamfanoninmu suke zargin mun amshi wadannan kudade mun kashe, Wanda ya jefa dayawanmu cikin zargi da rashin yarda a tsakaninmu dasu.

Don haka muke rokon wannan gwamnati data taimaka ta fiddamu wannan mawuyacin hali da muke ciki, mun sani cewa wannan kudin ba komai bane wajan gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here