BABBAN SHUGABA
1. Yau Juma’ar karshe muke,
A Rabi’u auwal dai muke,
A wata na samun shugaba.
2. A watan fa Mauludi muke,
Kaunar Habibi mun rike,
Mahmudu babban shugaba.
3. Ya dan Amina Mujtaba,
Kaunarka ita ce kan gaba,
Mai binka shi ke yin gaba,
4.Baban Batula Dahira,
Angon Khadija munawirra,
Babansu Muhsin Shugaba.
5. Ya shugaban duk duniya,
Ita kanta fadin duniya,
Anyi ta ne don shugaba.
6. Allah ina rokon ka ni,
Don Daha mai kyawon gani,
Lumuranmu duk ka shige gaba.
Ibrahim Hamisu
27- Rabiu Auwal-1441 H.
13-11-2020