Rundunar sahel sanity ta kashe mutun daya ta kubutar da yara biyu a zamfara da katsina

0

Rundunar sahel sanity ta kashe mutun daya ta kubutar da yara biyu a zamfara da katsina

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Rundunar Sojojin Operation Sahel Sanity sun kashe wani dan bindiga sun kubutar da wasu yara mata biyu a jihohin Zamfara da Katsina a ci gaba da kokarin kawar da ‘yan ta’addar daga arewa maso yamma da sauran masu aikata laifuka.

Hakan ya fitone cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mukaddashin Daraktan yada labarai take hedikwatar tsaro ta kasa,Brig. Janar Bernard Onyeuko , aka kuma rabata ga manema labarai.

Ya kara da cewa Sojojin Operation Sahel Sanity sun tsananta kai hare-hare kuma suna ci gaba da samun nasarori kan ‘yan bindiga da masu satar shanu da garkuwa da mutane.

Onyeuko ya ce a ranar 12 ga Nuwamba, sojoji yayin da suke sintiri a gefen dajin Wuta da ke jihar Katsina sun yi artabu da ‘yan fashi a kan babura wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani ‘dan fashi da kuma wasu da dama da suka ji rauni.

“Bayan artabun, an fatattaki ‘yan fashi kuma guda daya ya rasa ranshi kuma an kama bindiga AK-47 dauke da harsasai 27 na 7.62mm , in ji shi.

Onyeuko ya kara da cewa, a ranar 11 ga watan Nuwamba, sojoji da aka tura Angwan Doka, yayin wani samame sun ceto wasu ‘yan mata 2 a kauyen Munhaye da ke cikin karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Ya ce”Binciken farko ya nuna cewa wasu da ake zargin ‘yan fashi ne suka sace mutane biyu a kauyen Dan Aji da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here