INEC za ta yi zaɓuɓɓukan cike gurabu 15 a ranar 5 ga Disamba

0
537

INEC za ta yi zaɓuɓɓukan cike gurabu 15 a ranar 5 ga Disamba

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yanke shawarar gudanar da zaɓuɓɓukan cike gurabu guda 15 da su ka rage a ranar 5 ga Disamba.

Babban Kwamishina kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe a hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya bayar a Abuja, ya na mai bayyana cewa an yanke shawarar hakan ne a taron da kwamitin ya yi a ranar Juma’a.

Ya ce daga cikin abubuwan da INEC ta duba har da zaman tuntuɓa da ta kan yi da masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe a duk bayan wata uku.

Ya ce hukumar ta sake nazarin yanayin tsaro da sauran matsaloli da su ka shafi zaɓuɓɓukan cike gurabun da za a yi a jihohi 11.

A ranar 22 ga Oktoba ne hukumar ta ɗage gudanar da zaɓuɓɓukan cike gurabun da ta shirya yi a ranar 31 ga Oktoba saboda yanayin tsaro da sauran matsalolin sauyin yanayi da ke addabar ƙasar nan.

Okoye ya tunatar da cewa hukumar ta sake zama a ranar 5 ga Nuwamba kuma ta sake nazarin halin da ake ciki.

Ya ce a zaman, hukumar ta yi la’akari da cewa daga cikin abubuwa da dama akwai ɓarnar kayan da aka yi a ofisoshin ta da ke ƙananan hukumomi wanda ya shafi wasu sassa inda za a yi zaɓuɓɓukan cike gurabun.

Ya ce, “Don haka, hukumar ta yanke shawarar ta tuntuɓi muhimman masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe kafin ta yanke shawarar sake saka ranar da za a gudanar da zaɓuɓɓukan.

“Hukumar ta tuntuɓi jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyi masu zaman kan su a ranar 10 ga Nuwamba, da kuma kafafen yaɗa labarai da kwamitin tuntuɓar hukumomin tsaro kan batun zaɓe, wato ‘Inter-Agency Consultative Committee on Election Security’ (ICCES) a ranar 11 ga Nuwamba.

“A ƙarshe, ta yi taro da kwamishinonin zaɓe na jihohi a ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba.

“Bisa ga waɗannan tuntuɓa da aka yi, hukumar ta yi amanna da cewa an samu ingantuwar samar da tsaro a jihohin da abin ya shafa sannan matsalolin yanayi ma sun ragu bakin gwargwado.

“Don haka, hukumar ta yanke shawarar ta gudanar da dukkan zaɓuɓɓukan da su ka rage a ranar Asabar, 5 ga Disamba.”

Babban kwamishinan ya ce INEC ta yi godiya kan goyon baya da fahimta da kuma haɗin kan da masu ruwa da tsaki da dukkan jama’a su ka ba ta a lokacin da ta ke shawarwarin sake saka ranar da za a yi zaɓuɓɓukan cike gurabum.

A cewar sa, an yi hakan a bisa yunƙurin da ake yi na sauya fasalin harkar zaɓe da kuma ƙoƙarin ganin an bada ma’ana da daraja ga ƙuri’un masu zaɓe.

Okoye ya kuma yi kira ga masu zaɓe da masu ruwa da tsaki a jihohin da za a yi zaɓuɓɓukan da su ci gaba da bada haɗin kai ga INEC a ƙoƙarin ta na gudanar da zaɓuɓɓuka masu inganci a yanayin tsaro mai kyau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here