AN ZABI SHUGABANNIN YAN JARIDU NA KAFAFEN INTENET RESHEN JIHAR KANO

0

AN ZABI SHUGABANNIN YAN JARIDU NA KAFAFEN INTENET RESHEN JIHAR KANO

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Ƙungiyar ƴan jaridu a kafafen Intanet reshen jihar Kano, sun zaɓi Hisham Habib a matsayin sabon shugaban ƙungiyar. Kafin zaɓen na Hisham Habib, shi ne babban Editan jaridar News Tunnel da ke shafin Intanet.

Da ya ke bayyana sunayen sababbin shugabannin da aka zaɓa jim kaɗan da kammala zaɓen, Abdullateef Abubakar Jos, wanda shi ne tsohon shugaban riƙon ƙwarya na ƙungiyar , ya bayyana Dawud Nazifi mawallafin jaridar Daily Focus a matsayin mataimakin shugaban ƙungiyar.

Sauran shugabannin da aka zaɓa sun haɗa da Yakubu Salisu mawallafin jaridar Metro Daily Nigeria a matsayin Sakatare, sai Abbas Yusha’u Yusuf mawallafin jaridar Nigerian Tracker a matsayin mataimakin Sakataren Ƙungiya.

Zainab Abdurrahman Mai Agogo daga WhiteBlood Multimedia masu shafin Kakaki24 ta zama ma’ajin ƙungiya, inda Mukhtar Yahaya Usman daga jaridar Kano Focus a matsayin Sakataren Kuɗi, sai kuma Muhammad Buhari Abba daga jaridar Labarai24 a matsayin mai binciken kuɗi na ƙungiyar.

Sababbin shugabannin za su jagoranci ƙungiyar tsahon shekaru uku masu zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here